Mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage ta soki mazan Najeriya inda tace basu iya soyayya da tarairayar mace ba.
Ta bayyana cewa, mazan Najeriya na da kyauta da kuma kwarjini amma basu iya tarairayar mace ba.
Tace mazan Najeriya sun kuma iya Kwalliya amma ita ba abinda take nema ba kenan.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya tafi kasar Gabon dan wakiltar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a wajan wani taro da za'a yi.
https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1918570696768168424?t=VJN-hvLr2ztVJ5rb_KX06Q&s=19
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai na jihar Katsina inda yake ziyara ta musamman.
A yayin ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a daren ranar Juma'a, Tauraron mawakin Siyasa Dauda Kahutu Rarara ya gabatarwa da shugaba Tinubu da matarsa, A'isha Humaira inda ta gaishe da shugaban kasar.
https://twitter.com/abdullahayofel/status/1918552250688975253?t=ujjnjfaaHXn-GJEWleawMw&s=19
Shugaba Tinubu dai ya ji dadin wakar da Rarara ya masa sosai.
Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC zata fara binciken tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL watau Mele Kolo Kyari.
Tare da kyari, akwai mutane 13 da suma za'a bincikesu wanda suka yi aiki tare dashi.
Wata majiya daga EFCC ta bayyana cewa, Tuni aka kama wasu daga cikin tsaffin ma'aikatan sannan ana kan bin sahun sauran dan suma a kamasu.
Majiyar tace sauran wadanda ake bincike tare da kyari sune:
Abubakar Yar’Adua, Mele Kyari, Isiaka Abdulrazak, Umar Ajiya, Dikko Ahmed, Ibrahim Onoja, Ademoye Jelili, da Mustapha Sugungun.
Sauran sune Kayode Adetokunbo, Efiok Akpan, Babatunde Bakare, Jimoh Olasunkanmi, Bello Kankaya da Desmond Inyama.
Ana zargin dai Kolo Kyari da ma'aikatansa sun sace kudaden da aka ware dan gyaran matatun man ...
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya na shirin kakaba dokar ta baci da dakatar da gwamnonin jihohin Benue da Zamfara saboda matsalar tsaro.
Tuni majalisar tarayya ta aikewa wadannan jihohi da majalisunsu wasikar gayyata kan su je su yi bayanin dalilin da zai hana kada a saka dokar tabaci a cikin jihohin nasu.
Wata kungiyar kare hakkin bil'adama me suna Guardians of Democracy and Rule of Law ce ta aikewa majalisar tarayya da bukatar hakan.
Kungiyar tace Gwamnonin wadannan jihohi sun kasa samar da tsaro ga al'ummarsu inda ta nemi majalisa ta kai dauki wadannan jihohin.
Majalisar dai ta tabbatar da aikewa da wannan bukata.
Wakar da shahararren mawakin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara yawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a ziyarar da ya kai jihar Katsina ranar Juma'a ta dauki hankula sosai.
A cikin wakar an ji Rarara yana hadawa hadda Yarbanci.
A yayin da yake wakar, an ga Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna tafawa Rarara.
https://www.tiktok.com/@mubeedabai/video/7499990461390572806?_t=ZM-8w2Z8lzNfFv&_r=1
https://twitter.com/AbbaM_Abiyos/status/1918528231256281299?t=67glgoHt45PaLFyb4oCNBw&s=19
Da yawa sun jinjinawa Rarara inda suka ce wakar ta yi dadi.
Dakataccen Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara ya dawo gida Najeriya bayan makonni 2 yana hutawa a kasashen waje.
Da misalin karfe 7 na yammacin Ranar Juma'a ne Fubara ya sauka a birnin Fatakwal na jihar Rivers.
https://twitter.com/thecableng/status/1918543339411919205?t=TlaLrwl97IM1QzdRXmbpXA&s=19
Rahotanni sun bayyana cewa, yayi hutunne a kasar Jamus.
Wata Sabuwa:Kungiyar dalibai ta kasa, NANS ta nisanta kanta da Comrade Atiku Isa wanda ake zargin dan shugaban kasa, Seyi da wasu manya a kasar nan sun ci zarafinsa tsce ita ba shugabanta bane.
Tace babu yadda za ayi shugaban dalibai ya rika tafiya shi kadai ba tare da wasu shuwagabannin suna mara masa baya ba, sannan babu wata kungiyar dalibai data shiga cikin wannan case din.
Kawai dai son kai ne irin nashi da kuma son bata sunan gwamnati watakila ma biyansa akayi kan wannan aiki.
Rahotanni sun bayyana cewa, an kama tsaffin shuwagabannin matatun man fetur da aka sauke satin daya gabata saboda zargin sace kudaden da aka ware dan gyaran mamatun man fetur din.
Matatun man fetur din sune Warri, Fatakwal da Kaduna.
Jimullar kudaden da ake zarginsu da sacewa sun kai Dala $2,956,872,622.36.
A matatar man fetur ta Fatakwal ana neman dala $1,559,239,084.36 a yayin da a matatar man fetur ta Kaduna ana neman dala $740,669,600 inda a matatar man Warri ana neman dala $656,963,938.
Hakanan wata Majiya tace an samu Naira Biliyan 80 a asusun daya daga cikin manyan ma'aikatan.
Ana dai zargin wadannan shuwagabannin da yaudarar 'yan Najeriya musamman game da gyaran matatar man Warri.