Ƙungiyar Kiristoci ta CAN Ta Nemi Haɗin Gwiwar Shiga Ayyukan Hisbah, Don Magance Baɗala
Ƙungiyar CAN Ta Nemi Haɗin Gwiwar Shiga Ayyukan Hisbah, Don Magance Baɗala
Daga Mustapha Abubakar
Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta nemi haɗin gwiwa da kuma samun cikakken damar shigar da membobinta cikin ayyukan hukumar Hisbah domin samun kyakkyawar dangantaka da haɗin kai a aiki.
Fasto Nuhu Sani, Sakataren CAN na ƙaramar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna, ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron bita na kwana ɗaya da hukumar Hisbah ta shirya a sakatariyar ƙaramar hukumar.
Fasto Sani ya ce tun da hukumar Hisbah ƙungiya ce ta addini da ke da alhakin kawar da miyagun ayyuka a cikin al’umma, ya zama dole a samu haɗin gwiwa da ƙungiyar Kiristoci domin cika wannan buri.
Sakataren ya lurantar da cewa Musulmai da Kiristoci suna zaune tare a wuri ɗaya, a don haka ya zama ...








