Saturday, December 13
Shadow
Hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya ta yi hasashen samun Gajimare da tsawa a fadin kasar

Hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya ta yi hasashen samun Gajimare da tsawa a fadin kasar

Duk Labarai
Hukumar sararin samaniya ta Najeriya, (NiMet) ta yi hasashen samun Gajimare da rana a wasu sassan Najeriya daga ranar Laraba har zuwa Juma'a. A sanarwar data fitar ranar Talata a Abuja, Hukumar tace za'a samu rana a jihohin Arewa daga ranar Laraba zuwa Juma'a. Tace amma za'a iya samun hadari a sararin samaniyar jihohin Kaduna, Adamawa, Sokoto, Kebbi, Zamfara da Taraba da kuma tsawa. Hakanan tace a jihohin Benue, Plateau, Niger, Kwara da Kogi ma abinda ake tsammanin zai faru kenan. A jihohin Delta, Cross River, Akwa Ibom, Rivers da Bayelsa kuma sun ce za'a samu hasken rana da safe inda suma ana tsammanin Hadari da tsawa. A jihohin Kebbi, Taraba, Borno da Adamawa kuwa hukumar tace za'a tashi ranar Alhamisbda tsawa.
Dodar Ta tabbata, Kowa ya shaida mulkin Adalci na Shugaba Tinubu dan haka 2027 zai zarce>>Ganduje

Dodar Ta tabbata, Kowa ya shaida mulkin Adalci na Shugaba Tinubu dan haka 2027 zai zarce>>Ganduje

Duk Labarai
Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Mulkin Adalci na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yasa 'yan jam'iyyar PDP ke ta komawa APC. Ya bayyana hakane a Asaba, babban birnin jihar Delta yayin karbar gwamnan jihar, Sheriff Oborevwori da ya koma APC. Ganduje yace cin zaben 2027 ya tabbata ga Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ya kuma ce akwai karin gwamnonin PDP da zasu koma APC.
Likitoci sun mana kadan matuka duk sun tsere kasashen waje>>Jihar Kwara ta koka

Likitoci sun mana kadan matuka duk sun tsere kasashen waje>>Jihar Kwara ta koka

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kwara ta koka da karancin Likitoci a jihar inda hukumomin jihar sukace duk likitoci da yawa sun tsere kasashen waje. Shugaban hukumar kula da asibitoci na jihar, Abdulraheem Abdulmalik ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Yace a yanzu likitocin da suke dasu guda 99 ne maimakon 180 zuwa 200 da jihar Ke bukata. Yace suna neman likitoci su dauka amma babu, yace a kwankin baya likitoci 3 da suka tsere daga jihar sun koma bakin aiki bayan da aka yi karin Albashi. Yace babbar hanyar magance wanan matsala itace a samu a rika daukar nauyin dalibai suna koyan aikin likitanci inda daga baya sai su dawo su yiwa jihar aiki.
Ra’ayinane ba tsoron EFCC ba yasa na koma APC, kuma idan dai ana son Najeriya ta dore a matsayin dunkulalliyar kasa sai an zabi Tinubu a 2027>>Okowa

Ra’ayinane ba tsoron EFCC ba yasa na koma APC, kuma idan dai ana son Najeriya ta dore a matsayin dunkulalliyar kasa sai an zabi Tinubu a 2027>>Okowa

Duk Labarai
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Ifeanyi Okowa da ya koma jam'iyyar APC daga PDP yace ba tsoron EFCC ne yasashi komawa APC ba. A baya dai Hukumar EFCC ta fara binciken Okowa akan zargin batan Naira Tiriliyan 1.3 wanda daga baya kuma sai gashi ya koma jam'iyya me mulki ta APC. Hakana a baya tsohon shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomhole ya taba fadar cewa duk dan siyasar da ya shiga APC an yafe laifinsa. Wannan yasa mutane ke tunanin cewa dalili kenan da Okowa ya koma APC, amma ya musata hakan. Ya kara da cewa, zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarat 2027 shine zai sa kasanan ta dore a matsayin dunkulalliyar kasa.
Idan kace zaka yi aikin Gwamnati tsakani da Allah a Najeriya na zaka kare da ko sisi ba>>Inji Shugaban Kungiyar kwadago, NLC, Joe Ajaero

Idan kace zaka yi aikin Gwamnati tsakani da Allah a Najeriya na zaka kare da ko sisi ba>>Inji Shugaban Kungiyar kwadago, NLC, Joe Ajaero

Duk Labarai
Shugaban kungiyar Kwadago, NLC, Joe Ajaero ya bayyana cewa, duk wanda yace zai zama m'aikaci na gari ya rika zuwa aiki kullun to ba zai tsira da ko sisi ba a cikin Naira dubu 70 din da ake biya a matsayin mafi karancin Albashi. Ya bayyana hakane a Abuja wajan wani taro da aka gudanar. Yace amma duk da Dubu 70 din ma bata isa, a haka wasu jihohin baa biyan dubu 70 din a matsayin mafi karancin Albashi. Yace ma'aikata da yawa sun samu ragi ne ma daga abinda suke karba kamin karin Albashin inda yace hakan ya farune saboda hauhawar farashin kayan abinci da kuma harajin da ake cirewa. Ya kara da cewa, wasu jihohin kuma Naira dubu 5 kawai suka karawa ma'aikatan.
MATASHIN DA GOBARA talakume shagonsa yanzun haka a garin jos ABBA TAYA Wanda gobarar ta faru a kasuwar TERMINUS Allah yatsare nagabaAllah kuma yamayar mai da alkairi

MATASHIN DA GOBARA talakume shagonsa yanzun haka a garin jos ABBA TAYA Wanda gobarar ta faru a kasuwar TERMINUS Allah yatsare nagabaAllah kuma yamayar mai da alkairi

Duk Labarai
INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJUUN. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} MATASHIN DA GOBARA talakume shagonsa yanzun haka a garin jos ABBA TAYA Wanda gobarar ta faru a kasuwar TERMINUS Allah yatsare nagabaAllah kuma yamayar mai da alkairi
Ana hasashen aƙalla shaguna sama da 100 sun ƙone ƙurmus ya yin da wata gobara ta tashi da tsakar dare a kasuwar Terminus da ke birnin Jos na jihar Filato

Ana hasashen aƙalla shaguna sama da 100 sun ƙone ƙurmus ya yin da wata gobara ta tashi da tsakar dare a kasuwar Terminus da ke birnin Jos na jihar Filato

Duk Labarai
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. An samu mummunar gobara da ta laƙume shagunan mutane da dama a babbar kasuwar Terminus a wani layi da ake ƙira da “Parlon Buhari” da ke Jos fadar gwamnatin jihar Filato a daren jiya. Ana hasashen aƙalla shaguna sama da 100 sun ƙone ƙurmus a gobarar.
Ka sauka daga Gwamnan jihar Delta tunda a jam’iyyar mu aka zabeka>>PDP ta gayawa Gwamna Sheriff bayan a ya koma APC, ta garzaya kotu

Ka sauka daga Gwamnan jihar Delta tunda a jam’iyyar mu aka zabeka>>PDP ta gayawa Gwamna Sheriff bayan a ya koma APC, ta garzaya kotu

Duk Labarai
Jam'iyyar PDP ta yi martani kan komawar Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori zuwa jam'iyyar APC. Shugaban jam'iyyar na riko, Ambassador Umar Damagum, ya bayyana cewa sun tafi kotu da neman Gwamna Sheriff ya sauka daa kujerar Gwamna tunda a karkashin PDP aka zabeshi. Yace a baya sun fuskanci matsalolin da suka fi wannan yawa kuma duk sun tsallake dan haka wannan wasan yara ne. Yace an baiwa Gwamnatin gudanarwa na yankin kudu maso kudu umarnin ya kula da jam'iyyar PDP a jihar ta Delta saboda duka 'yan jam'iyyar a jihar sun canja sheka.
A dakin Otal Muka kama Nnamdi Kanu yana hutawa da wata mata>>Gwamnatin Tarayya

A dakin Otal Muka kama Nnamdi Kanu yana hutawa da wata mata>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
A ci gaba da shari'ar da ake tsakanin shugaban kungiyar dake son kafa kasar Biafra, IPOB, watau Nnamdi Kanu da gwamnatin tarayya, Gwamnatin tarayya ta gabatar da shaidarta na farko. Lauyan Gwamnatin tarayya ya nemi shaidar ya rufe fuska saboda tsaro kuma Alkalin dake shari'ar ya amince da hakan hakana shima lauyan Nnamdi Kanu bai kalubalanci hakan ba. Shaidar ya bayyana fuska a rufe inda yace shine ya jagoranci jami'an tsaro zuwa dakin da Nnamdi Kanu yake a Otal. Ana zargin Nnamdi Kanu da cin amanar kasa, da aikata ayyukan ta'addanci.
Idan dai za’a yi zaben gaskiya, Peter Obi baya bukatar Atiku ko El-Rufai kamin ya kayar da Tinubu>>NLC

Idan dai za’a yi zaben gaskiya, Peter Obi baya bukatar Atiku ko El-Rufai kamin ya kayar da Tinubu>>NLC

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta bayyana cewa, idan dai za'a yi zaben gaskiya, Peter Obi baya bukatar Hada kai da Atiku Abubakar ko El-Rufai kamin yayi nasara kada Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027. Mataimakin shugaban NLC ne ya bayyana hakan inda yace a zaben 2023, Peter Obi ya kama hanyar nasara kamin a samu tangardar da ta canja lamarin. Yace indai hukumar zabe me zaman kanta, INEC ba zata yi Magudi ba, to Peter Obi yana da karfin mabiyan da zai lashe zaben 2027.