Friday, December 5
Shadow
Jam’iyyar PDP ta kori Nyesom Wike

Jam’iyyar PDP ta kori Nyesom Wike

Duk Labarai
Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta sanar da korar ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu jiga-jiga daga cikinta, saboda abin da ta kira yi wa jam'iyya zagon-ƙasa. Cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ta ɗauki matakin ne domin kawo haɗin kai da ladabtarwa a jam'iyyar da kuma mayar da hankali ga zaɓukan 2027 masu zuwa. Sauran mutanen da jam'iyyar ta kora sun haɗar da Samuel Anyanwu da Kamaldeen Ajibade da Ayo Fayose da Austin Nwachukwu da kuma wasu. Sanarwar ta ce matakin ya samu amincewar mafiya rinjayen wakilan jam'iyyar da ke halartar babban taronta na ƙasa da ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Kalli Bidiyo: Kungiyar Tsaffin Sojojin Najeriya sun yi kira ga shugaba Tinubu ya sauke Wike daga mukamin Minista

Kalli Bidiyo: Kungiyar Tsaffin Sojojin Najeriya sun yi kira ga shugaba Tinubu ya sauke Wike daga mukamin Minista

Duk Labarai
Kungiyar Tsaffin Sojojin Najeriya ta nemi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya sauke Ministan Babban birnin tarayya, Abuja Nyesom Wike daga mukamin Minista. Kungiyar tace Wike na takawa da wulakanta mutane da yawa inda ta nemi ko da ba'a saukeshi ba a canja masa ma'aikata. https://twitter.com/emmaikumeh/status/1989732131309064632?t=uEsh6BIihZvXReiaXN7o_Q&s=19 Hakan na zuwane bayan da Wike yayi dambarwa da sojan Ruwa, AM. Yerima akan wani fili da akw rigima akanshi a Abuja.
Kalli Bidiyo: Gwamnan Katsina, Dikko Raddah na shan suka bayan da yace Likitocin Najeriya basu da kishi suna fita aiki kasashen waje maimakon su tsaya Najeriya su taimakawa ‘yan uwansu

Kalli Bidiyo: Gwamnan Katsina, Dikko Raddah na shan suka bayan da yace Likitocin Najeriya basu da kishi suna fita aiki kasashen waje maimakon su tsaya Najeriya su taimakawa ‘yan uwansu

Duk Labarai
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Raddah ya bayyana rashin jin dadinsa kan yanda likitoci ke tserewa daga Najeriya suna zuwa kasashen waje aiki. Gwamnan yace abin takaici shine a baya likitoci mata daga Najeriya basa fita kasashen waje yin aiki amma a yanzu likitoci mata daga Arewa suma sun bi sahu. Yace irin wadancan kasashe mutanensu ragwayene basa iya karatun aikin Likita shiyasa suke zuwa su baiwa likitocin Najeriya Albashi me tsoka dan su daukesu. Ya zargi Likitocin da rashin kishin al'ummarsu. https://twitter.com/Yantumakii/status/1989583505148244410?t=JOBFJyaDyxiUrKcFDCejIA&s=19 Saidai hakan ya jawowa Gwamnan suka inda wasu ke cewa ba'a kula da hakkokin Likitocin ne sannan ba'a biyansu albashi me kyau shiyasa.
Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Bashir Ahmad yayi kira ga shugaba Tinubu da ya kawo Cristiano Ronaldo da sauran ‘yan kwallon kasar Portugal Najeriya dan ya farantawa ‘yan Najeriya rai kamin zaben 2027

{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya kawo Tauraron kwallon kafa, Cristiano Ronaldo da sauran 'yan kwallon kasar Portugal Najeriya su yi wasa. A cewarsa, hakan zai taimaka matuka wajan farantawa 'yan Najeriya rai musamman kamin zaben shekarar 2027. Malam Bashir yace dalilinsa shine mafi yawan 'yan Najeriya masoya Cristiano Ronaldo ne. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1989666298368806928?t=G41IOdMFl1Greu_oy...
Kalli Bidiyo: Yanda ‘yansanda suka kama Malamin Coci me mukamin Reverend Father da Muqqan Maqamai a jihar Filato

Kalli Bidiyo: Yanda ‘yansanda suka kama Malamin Coci me mukamin Reverend Father da Muqqan Maqamai a jihar Filato

Duk Labarai
Wannan wani Bidiyo ne da ya nuna yanda Hukumar 'yansandan Najeriya ta kama wani malamin coci me mukamin Reverend Father a jihar Filato da muggan makamai. An ji jami'in 'yansandan na ce masa, yau malam addu'ar ka bata yi aiki ba. Bidiyon dai tsohon Bidiyo ne amma wasu 'yan Najeriya ke kara yadashi saboda cewar da shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi zai kawo Khari Najeriya suke kira a gareshi ya ga irin abinda ke faruwa. https://twitter.com/abdullahayofel/status/1989633605975396488?t=mWJzy6Hu59e5G0RW3cx_Tw&s=19
Kalli Bidiyon:Karka yadda ka Nemi Amaryarka a Daren Farko, ka bari sai an kwana 6 dan kada ta renaka taga a yunwace kake>>Inji Wannan

Kalli Bidiyon:Karka yadda ka Nemi Amaryarka a Daren Farko, ka bari sai an kwana 6 dan kada ta renaka taga a yunwace kake>>Inji Wannan

Duk Labarai
Wannan mutumin ya dauki hankula bayan da ya bayar da shawarar cewa, kada Angwaye su yadda su nemi Amarensu a daren farko da aka kai musu. Yace Mutum ya hakura sai bayan kwanaki 5 zuwa 6 dan kada amaryar ta renashi tace dama a yunwace yake da saduwar. https://www.tiktok.com/@al_sudais.md6671/video/7572166175002660103?_t=ZS-91QFPaC7D4T&_r=1
Kalli Bidiyo: Muna gani Ake daukar ‘ya’yanmu ana aikata Alfasha dasu saboda Talauci ba yanda muka iya>>Inji Wannan baiwar Allahn

Kalli Bidiyo: Muna gani Ake daukar ‘ya’yanmu ana aikata Alfasha dasu saboda Talauci ba yanda muka iya>>Inji Wannan baiwar Allahn

Duk Labarai
Wannan baiwar Allahn ta jinjinawa tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso inda tace ya taba taimaka mata da jarin Naira dubu 10. Tace amma yanzu tana bukatar Tallafi, tace matan aure na bukatar Tallafi. Ta bayar da labarin yanda tace akewa 'ya'yansu mata Fyadhe kuma duk takauci ne ya kawo hakan. https://www.tiktok.com/@mblawan10/video/7572211932082507029?_t=ZS-91QEX6WIvoW&_r=1
Kalli Bidiyo: Sojan Najeriya yayi gargadin cewa ida aka sake aka kori Sojan Ruwa, AM. Yerima daga aiki, za’a ga abhinda Zhasuyi a kasarna

Kalli Bidiyo: Sojan Najeriya yayi gargadin cewa ida aka sake aka kori Sojan Ruwa, AM. Yerima daga aiki, za’a ga abhinda Zhasuyi a kasarna

Duk Labarai
Sojan Najeriya ya bayyana cewa masu kiran a kori Sojan ruwa, AM. Yerima daga aiki, su jira su ga abinda zai faru idan hakan ta faru. Yace ba zai yiyu Janar ya bayar da umarni ba wani Dan siyasa yace kada abi wannan umarnin ba. https://twitter.com/General_Somto/status/1989027173659730321?t=ocG686SlrNHmBopm3mhWdQ&s=19 Hakan na zuwane bayan dambarwar data faru tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da Sojan Ruwa, AM. Yerima bayan da sojan ya hana Wike Shiga wani fili a Abuja.