Thursday, May 14
Shadow
Yanda jigon jam’iyyar APC daga jihar Kano ya rasu a Otal din Abuja

Yanda jigon jam’iyyar APC daga jihar Kano ya rasu a Otal din Abuja

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, mataimakin sakataren jam'iyyar APC ta jihar Kano, Abdulsalami Ginsau ya rigamu gidan gaskiya a otal din Chida dake Utako, Abuja. Rahoton yace Abdulsalami shine ke kula da masaukin baki na wakilan jam'iyyar APC daga jihar Kano a babban taron jam'iyyar da aka yi a Abuja. Kuma ya je otal din inda kama duka dakunan otal din guda 150. Saidai bayan da gari ya waye aka tafi wajan taron jam'iyyar APC din sai ba'a ganshi ba, anan aka fara bincike. Shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ya bayyana cewa, sun kai korafi ofishin 'yansanda dake Utako, yace sai 'yansandan suka ce an kawo musu rahoto daga Otal Chida, ko da suka je sai suka ga Abdulsalami ne. 'yansanda sun ce sun fara bincike kan lamarin. Itama wata majiya daga otal din ta tabb...
Kalli Bidiyon: Matasa Musulmai na Jis na shan yabo saboda yanda suka rika boye Kiristoci yayin da Rikici ya barke, daga baya suka rika mikasu hannun jami’an tsaro

Kalli Bidiyon: Matasa Musulmai na Jis na shan yabo saboda yanda suka rika boye Kiristoci yayin da Rikici ya barke, daga baya suka rika mikasu hannun jami’an tsaro

Duk Labarai
Bidiyo kala-kala na ta yawo a kafafen sada zumunta inda aka ga Musulmai a Jos na boye Kiristoci a yayin da rikici ya barke. An ga yanda daga baya suke mika Kiristocin a hannun jami'an tsaro. https://twitter.com/i/status/2039355260716589252 Lamarin ya jawo musu yabo da kuma Addu'ar Allah ya kawo mana zaman Lafiya. https://twitter.com/i/status/2039395012455084293
Babban yaron tsohon Ministan tsaro, Abubakar Badaru ya fice daga jam’iyyar APC

Babban yaron tsohon Ministan tsaro, Abubakar Badaru ya fice daga jam’iyyar APC

Duk Labarai
Daya daga cikin manyan yaran tsohon Ministan tsaro, Abubakar Badaru me suna Hon. Zakari Kafin Hausa ya fice daga jam'iyyar APC. A sakon da ya fitar dake ta yawo a kafafen sada zumunta yace ya fice daga jam'iyyar APC saboda tana saka mutane cikin damuwa. Sannan yayi kira ga duka mabiyansa suma su fice daga jam'iyyar. https://twitter.com/i/status/2039457227031900603
Dalilin da yasa duk da zuwan sojojin Amurka Najeriya ba’a fara ganin habakar tsaro ba>>Injin Hukumar sojoji Najeriya

Dalilin da yasa duk da zuwan sojojin Amurka Najeriya ba’a fara ganin habakar tsaro ba>>Injin Hukumar sojoji Najeriya

Duk Labarai
Hukumar sojojin Najeriya ta baiwa 'yan Najeriya hakuri saboda rashin ganin canji a harkar tsaro duk da zuwan sojojin Amirka. Me magana yawun hukumar Major General Micheal Onoja ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai. Yace sojojin na Amirka suna aikin bayar da bayanan sirri ne amma basa yaki. Yace 'yan Najeriya su yi hakuri sai a hankali za'a fara ganin Chanji.
Da Duminsa: Na fasa ziyarar da na yi niyyar kaiwa jihar Ogun, saboda abinda ya faru a jihar Filato>>Inji Shugaba Tinubu

Da Duminsa: Na fasa ziyarar da na yi niyyar kaiwa jihar Ogun, saboda abinda ya faru a jihar Filato>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya fasa kai ziyarar da yayi niyyar yi zuwa jihar Ogun saboda abinda ya faru a jihar Filato. Yace a yanzu zai kai ziyara jihar Filato ne dan jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa dasu sannan ya basu tabbacin samar da tsaro. Yace daga can zai wuce Legas dan yin hutun good Friday sannan kuma zai yi ziyarar aiki a Lagos din da Ogun da Bayelsa.
Jam’iyyar ADC ka iya samun Tangarda: Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta cire Shugaban ADC na rikon kwarya da sakataren jam’iyyar na Rikon Kwarya daga shafinta

Jam’iyyar ADC ka iya samun Tangarda: Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta cire Shugaban ADC na rikon kwarya da sakataren jam’iyyar na Rikon Kwarya daga shafinta

Duk Labarai
Hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta sanar da cire shugaban jam'iyyar ADC na rikon kwarya, David Umahi da sakataren jam'iyyar na rikon kwarya, Rauf Aregbesola daga shafinta na tattara bayanan shuwagabannin jam'iyyun Najeriya. INEC tace ta yi hakanne saboda karar da aka shigar a kotun daukaka kara daga wani bangare na jam'iyyar da basu yadda da shugabancin su David Mark ba. Kwamishinan yada labarai na INEC, Mohammed Kudu Haruna ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, yace zasu dakata har sai sun ji hukuncin da kotun daukaka karar zata yanke. Wanda ya shigar da karar shine Nafiu Bala Gombe wanda ke ikirarin cewa shine shugaban jam'iyyar ta ADC.
Hukumomi sun kori baturen kasar Amurka da ya shigo Najeriya yake tunzura Kiristoci akan Musulmai

Hukumomi sun kori baturen kasar Amurka da ya shigo Najeriya yake tunzura Kiristoci akan Musulmai

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumomin Najeriya sun kori dan kasar Amirkar nan me suna Mr. Alex Barbir wanda ya shigo Najeriya yake tunxura Kiristoci akan Musulmai. Malam Bashir Ahmad wanda tsohon Hadimin shugaban kasa ne ya bayyana hakan ta shafisa na X inda yace wata majiya me karfi ta sanar dashi hakan. https://twitter.com/i/status/2039371038832603359 A baya dai, an yi kiran Hukumomin su dauki mataki akan wannan bature da ba'a amince da salon da ya shigo dashi Najeriya ba.