Friday, December 5
Shadow
An baiwa ‘Yan Kwallon Najeriya kyautar Dala $120,000 bayan nasarar 4-1 da suka samu akan Kasar Gabon jiya

An baiwa ‘Yan Kwallon Najeriya kyautar Dala $120,000 bayan nasarar 4-1 da suka samu akan Kasar Gabon jiya

Duk Labarai
Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya da hadin gwiwar wasu kamfanoni masu zaman kansu, sun baiwa kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles Kyautar dala $30,000 akan kowace kwallo daya da suka ci, kamar yanda hukumar ta yi Alkawari. An basu wadannan kudaden a dakin canja kaya bayan kammala wasan. Kudin zasu kama jimullar Dala $120,000 kenan tunda kwallaye 4 'yan kwallon suka ci Gabon jiya. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1989341403743473669?t=PzA1PhpB30K0p8NJETDCqw&s=19
Kalli Bidiyo: Duk da Bidiyon da ya watsu kowa yaga abinda ya faru, Wike ya ce karya ake masa bai Zhagi Sojan Ruwa AM Yerima ba

Kalli Bidiyo: Duk da Bidiyon da ya watsu kowa yaga abinda ya faru, Wike ya ce karya ake masa bai Zhagi Sojan Ruwa AM Yerima ba

Duk Labarai
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, karya ake masa bai zagi sojoji ba a karawarsa da sojan Ruwa, AM. Yerima. Wike ya bayyana hakane a ganawa da manema labarai inda ya fadi cewa ya tallafawa ayyukan jami'an tsaro a matsayin Ministan Abuja da yayi. Saidai Sanata Dino Melaye ya bayyana mamaki da jin abinda Wiken yake fada. https://twitter.com/_dinomelaye/status/1989321220186091774?t=qXOAiy_fMZ_s0x7gov8G8A&s=19
Kalli Bidiyo: Ya zargi cewa, Saboda Naira Dubu 8 da rashin iya aiki, Asibiti a Abuja sun bar Jaririnsa ya Koma ga Allah

Kalli Bidiyo: Ya zargi cewa, Saboda Naira Dubu 8 da rashin iya aiki, Asibiti a Abuja sun bar Jaririnsa ya Koma ga Allah

Duk Labarai
Wannan mutumin Yayi zargin cewa, Wani Asibiti a Abuja ya bari jaririnsa ya mutu saboda rashin iya aiki da kuma Naira dubu 8. A Bidiyon da ya wallafa, an ganshi yana kuka a gaban asibitin yana zarginsu da rashin iya aiki da daukar 'yan Arewa aiki. https://www.tiktok.com/@talk2davic/video/7572121131570728199?_t=ZS-91OQ4G8xWG8&_r=1
Ni Dai da in Aikata Alfasha da Me Bakin Kyss wallahi gara Inyi Khadari abuna ya guntule>>Inji Ustaz Hussaini a yayin da suke musayar kalamai tsakaninsa da me bakin Kiss

Ni Dai da in Aikata Alfasha da Me Bakin Kyss wallahi gara Inyi Khadari abuna ya guntule>>Inji Ustaz Hussaini a yayin da suke musayar kalamai tsakaninsa da me bakin Kiss

Duk Labarai
Malam Dr. Hussain Kano dake fadakarwa a kafafen sada zumunta ya mayarwa da Me Bakin Kiss martani bayan zagin da ta yi masa. Malam yace yana mamakin mazan dake nemanta inda ya zargeta da kazanta. Kalli Bidiyon jawabinsa anan: https://www.tiktok.com/@dr.hussainkano5/video/7572492094338518328?_t=ZS-91OMOYZQMN6&_r=1
Kalli Bidiyo: Kirista ‘yar Jihar Borno ta zargi cewa Tunda Gwamna Zulum ya hau Mulki, Addininsa na Musulunci kadai da musulmai kadai yake taimakawa ba ya taimakawa Kiristoci

Kalli Bidiyo: Kirista ‘yar Jihar Borno ta zargi cewa Tunda Gwamna Zulum ya hau Mulki, Addininsa na Musulunci kadai da musulmai kadai yake taimakawa ba ya taimakawa Kiristoci

Duk Labarai
Wannan wata Kiristace da ta bayyana cewa, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum Musulmai da musulinci kadai yake taimakawa. tace baya taimakawa Kiristoci inda tace haka suke hada kudi su ginda coci amma a kona musu. Ta kuma zargi Gwamnan da yafewa 'yan Bìndìgà wanda tace daga baya suke zuwa su kara yiwa mutane tà'àddànci. https://www.tiktok.com/@ryma5570769784231/video/7572488734541614348?_t=ZS-91OLSctBVa4&_r=1
Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Duk Labarai
Shugaba Tinubu Ya Sabunta Nadin Buba Marwa A Matsayin Shugaban Hukumar NDLEA Har Na Tsawon Shekaru Biyar Shugaba Bola Tinubu ya sabunta nadin Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa Mai Ritaya, a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) na tsawon wa’adin shekaru biyar, a cewar wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja ranar Juma’a. Marwa, wanda aka fara nada shi a shekarar 2021 a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi aiki a baya a matsayin Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Kawar da Shan Miyagun Kwayoyi tsakanin 2018 da 2020. Sabon nadin zai kai tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar har zuwa shekarar 2031. Marwa wanda ya kasance tsohon gwamnan jihohin Lagos da Borno, ya samu horon soja a Nigerian Military School da ...
Baka isa kace min in baiwa Sojan Ruwa, AM. Yerima hakuri ba, kai ta ka taba baiwa sojan ka Umarnin ya Shyekye ni>>Wike ya gayawa Buratai

Baka isa kace min in baiwa Sojan Ruwa, AM. Yerima hakuri ba, kai ta ka taba baiwa sojan ka Umarnin ya Shyekye ni>>Wike ya gayawa Buratai

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya mayarwa da Tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buhari martani kan kira da yayi a gareshi da ya baiwa Sojan ruwa, hakuri kan zagin da ya masa. Wike yace Buratai bai isa ya koyar dashi wani abuba dan a zaben 2019 yasa sojansa yayi magudin zabe dan ya kayar dashi zaben gwamna a jihar Rivers amma bai yi nasara ba. Yace hakanan kuma Buratai ya taba cewa, Dogarinsa ya Shekye shi amma bai samu nasarar yin hakan ba, yace dan haka bai isa yasashi ya bayar da hakurin ba. Wike yace zai ci gaba da zamarwa makiyansa kadangaren bakin tulu.
Abin takaici, Kasar China ce kadai cikin kasashen Duniya ta nuna da gaske tana tare da Najeriya tun bayan Bharazanar Amurka

Abin takaici, Kasar China ce kadai cikin kasashen Duniya ta nuna da gaske tana tare da Najeriya tun bayan Bharazanar Amurka

Duk Labarai
Rahotanni sun nuna cewa, kasar China ce kadai ta nuna da gaske take tana tare da Najeriya bayan barazanar da kasar Amurka ta yi na shigowa Najeriya dan yakar wadanda ta kira da cewa sunawa Kiristoci Khisan Kyiyashi. Kasar China ta nuna tana tare da Najeriya ne saboda tana da karfin dangantaka ta tattalin Arziki a Najeriya kuma Amurka zata zo ne dan ta lalata wannan dangantakar. Abin mamaki shine ko kasar Ingila da ta reni Najeriya bata nuna goyon baya ga Najeriya ba. Saidai kungiyar hadin kan kasashen Turai EU ta nuna cewa a girmama kasancewar Najeriya a matsayin kasa me zaman kanta, wanda hakan na jeka nayi kane. Kasar Saudiyya da sauran kasashen Larabawa wadanda su ma suna da dangantaka me karfi da kasar Amurka sun kasa fitowa su nuna suna tare da Najeriya duk da yawan musul...