Me magana da yawun shugaban kasa ya nemi a zartar da hukuncin ķķìsà kan matashiya ‘yar bautar kasa data soki Gwammatin Tinubu
Rahotanni sun bayyana cewa, me taimakawa shugaban kasa kan yada labarai, Temitope Ajayi ya nemi a zartar da hukuncin kisa kan matashiya Ushie Uguamaye saboda sukar da tawa shugaba Bola Ahmad Tinubu.
Kafar peoplesgazette ce ta wallafa cewa Temitope Ajayi ya nemi a yankewa Ushie hukuncin kisa saboda yace a zartar mata hukunci mafi tsanani da hukumar bautar kasa ta NYSC ta tanadar.
Saidai a bayaninsa, Ajayi, ya bayyana cewa, shi ba haka yake nufi ba, an canja masa manufar bayaninsa ne dan cimma wani buri.
Yace abinda yake nufi da zartarwa da Ushie hukunci mafi tsanani a dokar NYSC shine a koreta daga aikin bautar kasar, yace shi a iya saninsa wannan ne hukunci mafi tsanani a dokar NYSC ba hukuncin kisa ba.
Lamarin Ushie ya dauki hankula sosai inda ciki hadda Atiku Abubakar, da Pet...








