Monday, April 6
Shadow
An kama ‘yan Arewa 89 a Kudu da sunan Wai Mahara ne, saidai ‘yansanda sunce ma’aikatan kamfanin Dangote ne

An kama ‘yan Arewa 89 a Kudu da sunan Wai Mahara ne, saidai ‘yansanda sunce ma’aikatan kamfanin Dangote ne

Duk Labarai
Wasu 'yan Arewa 89 da aka kama a Legas da zargin cewa mahara ne, hukumar 'yansandan Najeriya ta fito tace ba mahara bane, ma'aikatan kamfanin Dangote ne. Hukumar 'yansandan Legas sun ce ma'aikatane aka kawo daga Katsina zasu yi aiki a matatar man fetur ta Dangote. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1923264289097281970?t=Ig44GRbIaAHgCrswQluiSg&s=19 Kakakin 'yansandan jihar Legas, CSP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da cewa sun gudanar da bincike kuma sun gano ma'aikatan matatar man Dangote daga Katsina ba mahara ba.
BUA ya yabawa Tinubu kan karyewar farashin kayan abinci

BUA ya yabawa Tinubu kan karyewar farashin kayan abinci

Duk Labarai
BUA ya yabawa Tinubu kan karyewar farashin kayan abinci Shugaban Kamfanin BUA , Abdulsamad Isyaku Rabiu, ya ce hangen nesa da shugaba Bola Tinubu ya yi wajen samar da rangwamen haraji kan muhimman kayan abinci a bara ya taimaka wajen karya farashin kayan abinci a Najeriya. Rabiu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawa da Shugaban Kasa a jiya Alhamis. “Farashin abinci yana raguwa a Najeriya kuma muna kokarin tallafawa wannan yunkuri. “Za ku tuna cewa mai girma Shugaban Kasa ya bayar da rangwamen haraji a bara domin a shigo da wasu kayan abinci kamar shinkafa, masara, alkama da dawa cikin ƙasa. “A lokacin, farashin abinci ya yi matuƙar tsada; farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 a bara ya kai kusan Naira 1...
Malamai A Faɗin Nijeriya Sun Fara Kiraye-Kirayen A Taka Wa Malama Juwairiyya Birki Saboda Salon Wa’azinta Yana Gurɓata Tarbiyya

Malamai A Faɗin Nijeriya Sun Fara Kiraye-Kirayen A Taka Wa Malama Juwairiyya Birki Saboda Salon Wa’azinta Yana Gurɓata Tarbiyya

Duk Labarai
Malamai A Faɗin Nijeriya Sun Fara Kiraye-Kirayen A Taka Wa Malama Juwairiyya Birki Saboda Salon Wa’azinta Yana Gurɓata Tarbiyya. Biyo bayan wa’azozin da ake zarĝiɲ Malama Juwairiyya take gabatarwa masu cike da labarai masu alaƙa da yâɗa fașãḍi da ɓarna cikin al’umma, wasu malamai a Najeriya sun fara kiraye-kirayen a takawa Malama Juwairiyya birki sabøda wa’azinta yana kama da gurɓâta tarbiyyar ƴaƴa mata da matan aure da ƴân mata, inji Malaman kamar yadda Dokin Karfe TV ta ruwaito suna cewa. A cewar ɗaya daga cikin matasan Malaman, Dakta Jamilu Aliyu, "Ke fășiƙâ ce, a gaban maza da mata an haɗa su a wajen Walima ki zo kina cewa wai kawai kuna tafiya sai ga wata azzâkãriɲ namiji na roba ya faɗo daga jakarta kika tsaya kina kallonta. Wannan labarin fa kina bayarwa ne Duniya tana kal...
Ba zamu bari ba, sai mun rama hare-haren da masu ikirarin Jìhàdì suka kawo mana>>Shugaban sojojin Najeriya ya sha Alwashi

Ba zamu bari ba, sai mun rama hare-haren da masu ikirarin Jìhàdì suka kawo mana>>Shugaban sojojin Najeriya ya sha Alwashi

Duk Labarai
Wani Kwamandan Sojojin Najeriya a Arewa maso gabas inda ake fama da karuwar hare-haren 'yan Bindiga na Bòkò Hàràm ya bayyana cewa ba zasu kyale ba, sai sun dauki fansa. A kalla sasanin sojoji 10 ne mayakan Bòkò Hàràm da ÌŚWÀP suka farmawa da hare-haren. Shugaban hedikwatar tsaro ta kasa, Christopher Musa ya bayyanawa sojojin cewa aka kokarin kai musu sabbin makamai kuma za'a magance matsalar ta tsaro inda ya karfafa musu gwiwa yayin ziyarar da ya kaiwa sojojin Borno.
Ban san ta yaya suke iya bacci ba yayin da ‘yan tà’àddà ke kàshè mutane>>Atiku ya koka kan matsalar tsaro, yace shuwagabannin da suka zo bayan mulkinsu shi da Obasanjo ne suka kawo matsalar tsaro

Ban san ta yaya suke iya bacci ba yayin da ‘yan tà’àddà ke kàshè mutane>>Atiku ya koka kan matsalar tsaro, yace shuwagabannin da suka zo bayan mulkinsu shi da Obasanjo ne suka kawo matsalar tsaro

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, shuwagabannin Najeriya da suka zo bayan Obasanjo ne ke da Alhakin dawowar Kungiyar Bòkò Hàràm. Ya bayyana hakane a Abuja a yayin ziyarar da wasu 'yan siyasa daga jihar Kogi suka kai masa. Yace kungiyar ta fara bayyanane a shekarar 2002 a jihar Yobe Yace suna sumun labari, Obasanjo ya aika aka kirashi yace mai ya yake ganin za'a bullowa wannan lamari? Sai yace masa a kira shuwagabannin tsaro a basu lokaci su gama da kungiyar, idan suka kasa sai a sauke su a nada wasu. Yace haka kuwa aka yi kuma aka murkushe kungiyar. Yace bayan sun sauka Mulki ne wanda suka hau suka yi sakaci kungiyar ta dawo.
Gwamnati ta bayyana jihohin da suka fi fama da tsadar kayan Abinci a Najeriya, Duba kaga jiharka na ciki?

Gwamnati ta bayyana jihohin da suka fi fama da tsadar kayan Abinci a Najeriya, Duba kaga jiharka na ciki?

Duk Labarai
Hukumar NBS dake kula da kididdigar alkaluma a Najeriya ta fitar da bayanan Alkaluma kasuwanci da kayan Masarufi na watan maris. Hukumar tace alkaluma sun nuna makin farashin kayan masarufi ya tsaya a mataki na kaso 23.71 cikin 100. Hakan na nufin farashin kaya masarufi sun yo kasa idan aka hada da alkaluma baya da aka samu. Saidai Jihohin Enugu, Kebbi, Niger, Benue, Ekiti, Nassarawa, Zamfara, Delta, Gombe, Sokoto, da babban birnin tarayya Abuja, nasu Alkaluman sama suka yi. Rahoton yace wadannan jihohi alkaluansu sun nuna suna da maki 30 cikin 100 na hauhawar farashin kayan masarufi.