Gwamnati tace zata siyar da gidajen da ta Kwace daga hannun tsohon Gwamnan baban bankin Najeriya, CBN
Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin sayar da gidaje 753 data kwace daga hannun tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele
Hakan na kunshene a cikin sanarwar da wakilin hukumar kula da gidaje ta Abuja, Salisu Haiba ya fitar a ranar Talata.
Ya bayyana cewa, sun karbi gidajen guda 753 daga hannun EFCC.
Yace mutane za'a sayarwa da gudajen.








