Tuesday, December 16
Shadow
Kasar Canada ta aikawa da kasar Amurka tallafin ma’aikata masu kashe gobara

Kasar Canada ta aikawa da kasar Amurka tallafin ma’aikata masu kashe gobara

Duk Labarai
Kasar Canada ta sanar da cewa ta aikawa kasar Amurka tallafin jiragen sama masu kashe Gobara a birnin Los Angeles. Koda a baya, kasar Mexico ma ta kaiwa kasar ta Amurka tallafin masu aikin kashe gobara. Jimullar masu kashe gobara dubu 14 ne ke aikin kashe gobarar. Rahotanni sun bayyana cewa, hadda masu laifi dake tsare a gidan yari sai da aka dauko dan su taimaka a kashe gobarar.
An gargadi gaba dayan mutane miliyan 10 dake zaune a birnin Los Angeles su shirya ficewa daga garin saboda Wata guguwa na shirin hura gobarar dake kan ci ta mamaye duka garin

An gargadi gaba dayan mutane miliyan 10 dake zaune a birnin Los Angeles su shirya ficewa daga garin saboda Wata guguwa na shirin hura gobarar dake kan ci ta mamaye duka garin

Duk Labarai
Rahotanni daga gobarar dake faruwa a birnin Los Angeles na kasar Amurka na cewa mahukunta sun sanar da duka mutanen dake zaune a birnin watau mutane miliyan 10 da su shirya ficewa daga cikinsa saboda wata guguwa ta doso garin tana niyyar hura wutar dake ci ta mamaye duka garin. Mahukunta sun ce suna kan shirin ko ta kwana na faruwar lamarin me cike da hadari. Zuwa yanzu dai gobarar ta kashe mutane 24 sannan ta kone gidaje sama da dubu 12 kuma ta tursasa mutane 100,000 barin gidajensu. Hakanan dukiyar da gobarar ta cinye ta kai dalar Amurka Biliyan 150.
Matar aure ta dabawa mijinta wuka ya mùtù bayan da ya zargeta da bin maza

Matar aure ta dabawa mijinta wuka ya mùtù bayan da ya zargeta da bin maza

Duk Labarai
Wata matar aure me suna Iyanu Adedeji 'yar kimanin shekaru 22 ta kashe mijinta me suna Funsho Jimoh dan kimanin shekarun 28. Lamarin ya farune a yankin Gbonogun dake Abeokuta jihar Ogun. Ma'auratan dai na da yara 2. Rashin jituwar ta farane bayan da mijin ya zargi matar tasa da vin amanarsa inda ta karyata, rikici ya kaure inda ta dakko wuka ta daba masa. Daga nan ne ta daukeshi zuwa asibitu inda likita ya tabbatar da ya mutu. Kakakin 'yansandan jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace wadda ake zargin tana hannu ana kuma ci gaba da abincike.
An zargi mutane 64 da yi wa wata matashiya fyaɗe a India

An zargi mutane 64 da yi wa wata matashiya fyaɗe a India

Duk Labarai
Wata matashiya ƴar shekara 18 daga jihar Kerala da ke kudancin Indiya ta zargi wasu maza 64 da yin lalata da ita tun tana da shekaru 13 da haihuwa. Ƴansanda sun kama mutane 28 da ake zargi da hannu a lamarin kawo yanzu - mutanen suna tsare kuma ba su yi wani bayani kan lamarin ba. Waɗanda ake tuhumar da ke da shekaru tsakanin 17 zuwa 47, sun haɗa da makwabtan matashiyar da kociyoyin wasanni da abokan mahaifinta, kamar yadda ƴansanda suka shaida wa BBC. Matashiyar ta ba da rahoton cin zarafin da ta ke zargin an yi ma ta ne bayan wata tawagar masu ba da shawara da ke aiki ƙarƙashin wani shiri na gwamnati sun ziyarci gidanta. Lauyan da ke jagorantar kwamitin kula da jin daɗin yara na gundumar, ya shaida wa jaridar Indian Express cewa matashiyar ƴar wasa ce kuma ta halarci sansanon...
Bama jin dadin yanda mutane suka fara yanke tsammani akan wutar lantarki ta Gwamnati suka koma samarwa kansu da wuta ta hanyar Sola>>Gwamnatin tarayya ta koka

Bama jin dadin yanda mutane suka fara yanke tsammani akan wutar lantarki ta Gwamnati suka koma samarwa kansu da wuta ta hanyar Sola>>Gwamnatin tarayya ta koka

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Gwamnatin tarayya ta koka kan yanda ake samun karuwan musamman kamfanoni da ma'aikatun gwamnati na samarwa kansu wutar lantarki inda suke dena amfani da wutar lantarki da gwamnati da kamfanonin rarraba wutar na Discos ke samarwa. A wani rahoto da hutudole ya kawo muku, kun ji cewa sama da kamfanoni da ma'aikatun gwamnati 200 ne suka daina amfani da wutar gwamnati suka koma samarwa kansu wutar lantarki, saboda tsadarta da kuma rashin tabbas. Da yake kokawa game da wannan lamari, m...
An gano wata hanyar da ‘yan ìndìgà ke amfani da ita dan samun màyàkà da yawa ta hanyar amfani da mata

An gano wata hanyar da ‘yan ìndìgà ke amfani da ita dan samun màyàkà da yawa ta hanyar amfani da mata

Duk Labarai
Shugaban rundunar sojojin Najariya, CDS, Christopher Musa ya bayyana cewa a yanzu 'yan Bindiga da yake babu wani gari dake hannunsu sun fito da dabarar samun mayaka. Yace a baya sukan kai hari garine su samu maza majiya karfi ko kana so ko baka so a tursasa maka ka dauki makami ka shiga cikinsu, idan ka kiya su yankaka. Yace amma yanzu basu da wannan damar. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Ya kara cewa, yanzu dabarar da 'yan Bindigar suke yi shine sukan samu mata su yi ta dirka musu ciki akai-akai suna haihuwa dan su yi amfani da yaran a matsayin mayaka. Yace idan sukawa mace ciki ta haihu, bayan wata 4 zasu sake saduwa da ita dan ta kara daukar wani cikin. Yace a kwanannan wasu 'yan Bindiga da suka mika wuya suka ajiye makamai su d...
Sai mun dauko hanyar nasara sai a rika cewa wai muna jefawa farar hula bamabamai suna kkashesu, ana yin hakane dan a kashe mana kwarin gwiwa da nuna cewa bamu san abinda muke ba>>Inji CDS, Christopher Musa

Sai mun dauko hanyar nasara sai a rika cewa wai muna jefawa farar hula bamabamai suna kkashesu, ana yin hakane dan a kashe mana kwarin gwiwa da nuna cewa bamu san abinda muke ba>>Inji CDS, Christopher Musa

Duk Labarai
Shugaban rundunar sojojin Najariya, CDS Christopher Musa ya bayyana cewa maganar a rika cewa suna kashe farar hila ta hanyar jefa musu bama-bamai yaudara ce da dabara dan a nuna cewa basu san abinda suke ba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV inda yace kamin su kai kowane hari, sai sun tabbatar da cewa akwai 'yan Bindiga a wajan, yace suna da shaidun bidiyo. Yace ba zasu ce ba'a rasa tsautsai na kashe farar hula ba, yace yawancin hakan na faruwane bayan sun kai hari kan maboyar makaman 'yan Bindigar. Yace shin ma wai me yasa sai idan sun fara samun nasara akan 'yan Bindiga ne sai a rika cewa suna kashe farar hula, kuma me yasa idan ance sun kashe farar hula, kamin su je wajan sai ace an binnesu, ba za'a bari su gudanar da bincike ba? Yayi z...
Matatar man fetur din Dangote da kamfanin man fetur na kasa, NNPCL sun samarwa kansu wutar lantarki inda suka daina amfani da wutar lantarkin Najeriya

Matatar man fetur din Dangote da kamfanin man fetur na kasa, NNPCL sun samarwa kansu wutar lantarki inda suka daina amfani da wutar lantarkin Najeriya

Duk Labarai
Yayin da wutar lantarkin Najeriya ta zama marar tabbas, kamfanoni da ma'aikatu 250 ne suka daina amfani da wutar da gwamnatin Najeriya da kamfanonin rarraba wutar na Discos ke samarwa inda suka koma samarwa kansu wutar. Mafi yawancin kamfanonin na amfani da wutar lantarkin sosai. Gashi Gas yayi tsafa, ga kudin wutar ana karba da yawa ga wutar ba tabbas shiyasa suka samarwa kansu mafita. A shekarar 2021, tsohon shugaban kaa, Olusegun Obasanjo shima ya dana amfani da wutar lantarkin Najeriya inda ya koma samarwa kansa wutar a dakin karatunsa dake Abeokuta jihar Ogun. Jimullar wutar da wadannan kamfanoni ke samarwa kansu ta kai karfin 6,500 megawatts wanda hakan ke nufin karfin wutar yafi wanda Gwamnatin Najeriya ke samarwa wadda ke da karfin 5,000MW a mafi akasari. Gwamnati tuni ...
Cocin Katolika tace yanzu ta amince ‘yan Lùwàdì zasu iya zama limamai a cikin cocin

Cocin Katolika tace yanzu ta amince ‘yan Lùwàdì zasu iya zama limamai a cikin cocin

Duk Labarai
Cocin Katolika ta yi canje-canje a dokokinta inda tace a yanzu dan luwadi zai iya zama limami a cocin me mukamin Priest. Saidai cocin tace kamar yadda doka take dolene ya zama ba zai rika yin luwadin ba saboda ba'a yadda Priest su rika saduwa ko wace iri ba. Wannan sabuwar dokar an yi ta a kasar Italiya ne saidai rahoton yace ba'a sani ko sauran kasashe suma zasu yadda da hakan ba. Limaman Cocin dai a baya sun yi fama da zarge-zargen luwadi musamman da kananan yara.