Thursday, December 18
Shadow
‘Yan Najeriya sun bayyana cewa man fetur din matatar man Dangote na dadewa kamin ya kare

‘Yan Najeriya sun bayyana cewa man fetur din matatar man Dangote na dadewa kamin ya kare

Duk Labarai
'Yan Najeriya da yawa ne suka bayyana jin dadinsu da amfani da man fetur din matatar man fetur ta Dangote. Da yawa da jaridar Punchng ta yi hira dasu sun ce sun ji dadin amfani da man fetur din na matatar man fetur ta Dangote saboda yana dadewa bai kone ba a mota idan aka kwatantashi da wanda suke amfani dashi a baya. Matatar man fetur ta Dangote ta bayyana cewa, ta yi hadaka da gidajen sayar da man fetur na MRS dan ta rika sayarwa 'yan Najeriya man fetur din da Rahusa. Wasu daga cikin wadanda aka yi hira dasu sun ce gwamnati ta yaudaresu kan matatar man fetur din Dangote inda suka ce man da ake shigowa dashi bashi da inganci.
Kotu ta bayar da belin Mahadi Shehu kan Milyan uku

Kotu ta bayar da belin Mahadi Shehu kan Milyan uku

Duk Labarai
Wata babbar kotun jihar Kaduna ta bayar da belin mai fafutuka Mahdi Shehu kan kudi Naira miliyan uku da kuma mutane biyu da za su tsaya masa a kan wannan kudi. Kotun ta ce wadanda za su tsaya wa dole ne su zama sanannun malamai a Nageriya. Sannan ta kwace fasfonsa kuma tace dolene sai ya rika zuwa wajan jami'an tsaro duk wata ana ganinsa, kuma duk idan ya zama dole sai yayi tafiya, ya sanar da kotun. Kotun tace ta amince ta bayar da belinsa ne saboda a yanzu ba'a tabbatar da laifin daya aikata ba.
Babu lungu da sakon da ba’a shaida salon Mulkina ba a Najeriya>>Shugaba Tinubu

Babu lungu da sakon da ba’a shaida salon Mulkina ba a Najeriya>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, babu lungu da sako na kasarnan da ba'a shaida salon mulkinsa ba a Najeriya. Shugaban ya bayyana hakane ta bakin me bashi shawara akan harkar sadarwa, Daniel Bwala a yayin da ake hira dashi a gidan talabijin na TVC. Bwala yace shugaba Tinubu a yayin da yazo kan mulki akwai jihohi kusan 19 dake fama da matsalar karancin kudi wanda cire tallafin man fetur da Tinubu yayi gwamnati ta samu karin kudin shiga sosai yasa jihohin suka farfado daga hanyar talaucewa da suka kama. Bwala ya kara da cewa, an samu ci gaba sosai kuma kowane lungu da sako na kasarnan sun shaida hakan. Yayi kira ga gwamnonin dasu tabbatar da sun bayar da ci gaban da ake bukata a jihohinsu.
Khalifa Aminu, fasihin yaron nan dan jihar Kano mai ƙere-ƙere, ya ƙirƙiri wata sabuwar na’ura mai nuna yanayin jini da jikin ɗan adam

Khalifa Aminu, fasihin yaron nan dan jihar Kano mai ƙere-ƙere, ya ƙirƙiri wata sabuwar na’ura mai nuna yanayin jini da jikin ɗan adam

Duk Labarai
. Ga bayanin na'urar nan da ya wallafa a shafin sa na Facebook. " Wannan shine sabon 'project' dina mai ban mamaki da ban al ajabi wato 'Scan blood & temperature device'. "Wato na'urar mai gano bugun jini da yanayin jiki. Wannan na'urar za ta iya temaka wa mutane da dama wajan kare lafiyar jikinsu. "Ita dai wannan na'urar ana saka ta a hannu ne. Bayan ka saka ta a hannu to duk inda ka shiga idan zafi yai yawa a wajen ko sanyi ko yanayin iskar da ka ke shaƙa to za tayi scaning din jikin ka ta ga yanayin 'temperature' din da jikin ka ya ke bukata idan wannan yanayin iskar ko zafi ko sanyi su kai yawa nan take za ta sanar da kai kabar wajen idan ba haka ba zaka iya cutuwa. "Sannan za ka iya scan din jinin jikin ka don ka ga lafiyar ka kalau ko ba ka da lafiya. " Wann...
An gano ƙanƙara mai shekara fiye da miliyan ɗaya a duniya

An gano ƙanƙara mai shekara fiye da miliyan ɗaya a duniya

Duk Labarai
Masana kimiyya a nahiyar Turai sun gano ƙanƙarar da watakila ake ganin ita ce mafi daɗewa a duniya a yankin Antarctica. Tawagar masu binciken ta haƙo silindar ƙanƙarar mai tsawon kusan kilomita uku wanda ke ɗauke da tsohon kumfa da kuma ɓurɓushi da aka daina ganin irinsa tun fiye da shekara miliyan guda. Masanan na fatan cewa yin nazarin tarihin yanayin zafi da matakan iskar gas zai taimaka musu wajen hasashen sauyin yanayi a nan gaba. Tuni dai masu binciken suka yayyanka ginshiƙin ƙanƙarar zuwa sassa masu tsayin mita ɗaiɗai domin faɗaɗa bincike a cibiyoyin bincike a faɗin nahiyar Turai.
Tinubu ya yi alhinin sojojin Najeriya da suka mùtù a harin Damboa

Tinubu ya yi alhinin sojojin Najeriya da suka mùtù a harin Damboa

Duk Labarai
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar dakarun ƙasar, da aka kashe a harin da mayaƙan Boko Haram ta kai wani sansanin soji da ke ƙauyen Sabon Gida, cikin ƙaramar hukumar Damboa a jihar Borno. Cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin ƙasar ta fitar, ta ce Tinubu ya jajanta wa rundunar sojin ƙasar sakamakon mutuwar dakarunta shida a harin. Haka kuma shugaban ƙasar, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya haddasa harin, domin ɗaukar matakan hana faruwar makamancinsa a nan gaba''. A ranar Asabar ne mayaƙan ISWAP suka ƙaddamar da hari da asuba kan sansanin sojin inda suka yi arangama da sojoji, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin ƙasar shida da mayaƙa fiye da 30. Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa sojojin ƙasar bisa jajirewar da suka yi, har ta k...
Za a ƙara kuɗin kiran waya a Najeriya – Gwamnatin Najeriya

Za a ƙara kuɗin kiran waya a Najeriya – Gwamnatin Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da shirin ƙara kuɗin kiran waya da na data, nan ba da jimawa ba. Ministan sadarwar ƙasar, Bosun Tijani ne ya bayyana haka a lokacin ganawa da masu ruwa da tsaki a Abuja. Ya ce hukumar sadarwa ta ƙasar, NCC ce za ta tsara yadda ƙarin zai kasance. Tijani ya ƙara da cewa, “Kafin mu zo da wannan shawara, sai da muka yi la'akari da abubuwa masu yawa na yadda hakan zai taimaka wajen gina ƙasarmu''. “Wasu daga cikin abubuwan sun haɗa da tabbatar da inganta hanyoyin sadarwarmu da inganta kamfanoninmu na cikin gida da tabbatar da ɗorewar kamfanonin kansu''. ''Haka ma kamar yadda muke ganin hauhawar farashin kayayyaki a duniya, su ma kamfannonin sadarwar na fuskantar wannan matsala, don haka ba za mu bari su durƙushe ba, dole mu yi wani abu don tabbatar ...
Ƴan sintiri sun ceto mutum 63 a hannun masu garkuwa a Sokoto

Ƴan sintiri sun ceto mutum 63 a hannun masu garkuwa a Sokoto

Duk Labarai
Tawagar ƴan sintiri a jihar Sokoto ta ce ta kuɓutar da mutum 63 daga hannun masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, a jihar mai fama da matsalar ayyukan ƴan bindiga. Wata sanarwa da ta samu sa hannun Garba Mohammed, mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar ta ce tawagar ta ƙunshi jami'an ƴansanda da jami'an tsaro ƙarƙashin gwamnatin jihar Sokoto. Bayanin ya bayyana cewa an kuɓutar da mutanen ne a tsawon kwana huɗu, daga ranar Lahadin da ta gabata. Sokoto na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya masu fama da matsalar ƴan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa. Haka nan a baya-bayan nan an samu ɓullar wata ƙungiyar ƴan bindiga da ake kira Lakurawa. Rundunar sojin Najeriya ta ce ta tsananta ayyukan yaƙar ƴan bindiga tun bayan ɓullar ƙungiyar ta...