Tinubu ya umarci a cire shingayen da ke kan iyakokin Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamitin shugaban ƙasa na musamman da zai cire dukkan wasu shingaye da ake da su a kan iyakokin ƙasar don sauƙaƙa harkokin cinikayya da tafiye-tafiye.
Amabasada Musa Nuhu wakilain Najeriya a ƙungiyar Ecowas ne ya sanar da hakan, a wata ziyara da ya kai iyakar Najeriya da Jamhuriyar Binin wato Same a ranar Laraba.
Masu ababen hawa sun sha kokawa da yadda ake karɓar kudade a hannunsu, a dukkan wani shinge da suka zo wucewa akan hanayr ta Iyakar ta Seme wato iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin.
Ambasada Nuhu ya ce "hanyar ta kasance wadda aka fi zirga-zirga a Afrika, musamman wajen fitarwa da shigar da kaya, da shige da ficen al'umma. Zamu iya ganewa idan ana tafiye tafiye ba tare da shinge ba a yankin Afrika ta Yamma", in ji shi.
"...








