Monday, December 15
Shadow

Maganin daina luwadi

Addu'a, Magunguna
Babban maganin daina Luwadi shine tsoron Allah. Alhamdulillahi tunda har Allah ya karkato da zuciyarka kake neman Maganin dena luwadi, wannan babban matakin hanyar shiriyane ka dauka wanda kuma idan Allah ya yarda Allah zai taimakeka akai. Babban Abin yi yanzu shine ka yi tuba na gaskiya da nadama ta gaske akan cewa, ba zaka sake komawa ga wannan bakar dabi'ar ba sannan ka yi addu'a sosai ta neman gafarar Allah domin Allah yana gafarta kowane zunubi matukar ba shirka bane aka mutu ana yi. Sannan ka roki Allah ya taimakeka wajan kokarin daina wannan dabi'ar. Hanyoyin Daina Luwadi Allah madaukakin sarki yana cewa, "Kace yaku bayina da kuka zalunci kawunanku(ta hanyar aikata zunubai, kada ku yanke tsammani daga rahamar Allah, lallai Allah yana gafarta duka zunubai, Lallai shin...

Maganin daina sata

Addu'a, Magunguna
Babban maganin daina sata shine tsoron Allah. Sata indai ba ta cuta bace wadda ita kuma matsayinta daban, mutum zai sawa ransa kudirin dainawa ne, da kuma tuba da mayar da abinda ya sata da yin nadama akan abinda ya aikata. Idan kuma mutum bai da halin mayar da abinda ya sata ga maishi, watau ko ya kare kuma baida dukiyar da zai mayar da madadinsa, kuma bai da karfin da zai je ya nema, watau yayi aiki ya samu kudi ya biya, to sai ya tuba ga Allah. Akwai sata ta cuta wadda a likitance ake kiranta da sunan Kleptomania. Ita wannan sata ta cuta tana da alaka da rashin lafiyar kwakwalwa, wanda suke da ita mafi yawanci masu hali ne kuma basu da yawa a Duniya, kuma sukan saci abinda sun ma fi karfinshi ko kuma babu abinda zai amfanesu dashi. Hakanan masana sunce ita irin wannan cutar...
Kasar Pakistan ta kaiwa Afghanistan hari inda mutane 46 suka mutu

Kasar Pakistan ta kaiwa Afghanistan hari inda mutane 46 suka mutu

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Pakistan na cewa, kasar Afghanistan ta kai mata hari da jiragen yaki na sama wanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 46. Wadanda suka mutun wanda yawanci matane da kananan yara kamar yanda gwamnatin kasar ta Afghanistan ta tabbatar. Hakanan akwai karin mutane 6 da suka mutu sanadiyyar karin wasu hare-haren da kasar ta Pakistan ta kai a kasar ta Afghanistan. Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Afghanistan tuni ta kira wakilin jakadan Pakistan dake kasarta inda ta yi Allah wadai da lamarin tare da shan Alwashin kai harin ramuwar gayya. Kafar Reuters tace kasar Pakistan ta kaiwa 'yan Bindigar TTP harine biyo bayan harin da suka kai a kudancin Waziristan daya kashe sojojin Pakistan din guda 16. TTP ta hada kai da Kungiyar Taliban amma tana kai harin...
Karanta Jadawalin Alkawuran da Gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi wanda bata cikasu ba a shekarar 2024

Karanta Jadawalin Alkawuran da Gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi wanda bata cikasu ba a shekarar 2024

Duk Labarai
A yayin da ya rage saura kwanaki kadan mu shiga shekarar 2024, mun kawo muku jadawalin alkawuran da Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta yi wadanda bata cikasu ba a wannan shekarar. Alkawarin cire haraji akan kayan Abinci Cire Haraji akan kayan Abinci dan samarwa talakawa hanyar saukin rayuwa abune da gwamatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta alkawarta ta bakin Ministan Noma, Abubakar Kyari. Yace za'a cire haraji akan Alkama, Shinkafa, Masara da sauransu dan samarwa mutane saukin rayuwa. A ranar 14 ga watan Augusta, Hukumar Kwastam ta sanar da izinin data samu daga fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dan cire tallafin. Hukumar kwastam tace cire harajin zai fara aiki ne daga 15 ga watan July zuwa 15 ga watan Disamba. Saidai da ba'a ga an cire harajin ba, an ...