Wannan wani Fasto ne da yayi Alkawarin mayar da ruwa giya inda yace mabiyansa su kawo ruwa da yawa suka kuwa kawo suka taru dan ganin abin mamaki.
Saidai Abu yaki yiyuwa inda faston saidai gumi kawai yake amma Ruwa yaki komawa giya.
Ka Mayarwa Da PDP Da Sauran Ma'aikatun Da Ka Karbe Musu Ofisoshinsu, Amma Ka Tabbatar Sun Biya Harajin Nan Da Makonni Biyu, Umarnin Tinubu Ga Ministan Abuja, Wike.
Gine-gine 4,794 ne aka samu da wannan laifi.
Saidai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ce a bude gine-gine da aka rufe saboda rashin biyan Harajin inda yace ya basu Kwanaki 14 su biya.
Wani me laifi me suna Benjamin Schreiber da ake tsare dashi a gidan yari na jihar Iowa dake kasar Amurka saboda aikata kisa aka kuma mai hukuncin daurin rai da rai yace a sakeshi yanzu ya gama zaman gidan yarinsa tunda ya mutu ya dawo.
Wata Kwaya ce ya sha ta sa yayi Doguwar suma shine da ya farfado ya shigar da kara yace wai a sakeshi tunda ya mutu ya dawo.
Alkali dai yayi watsi da wannan bukatar tashi inda yace har yanzu yana nan da ranshi be mutu ba.
Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ya sha Alwashin karya farashin Shinkafa inda yace zai kafa kamfanin shinkafar a jihar Naija.
Hakan na zuwane kwanaki bayan da BUA ya sha Alwashin karya farashin shinkafar.
Babbar me baiwa shugaban kamfanin na Dangote shawara Fatima Abdurrahman ce ta bayyana haka inda tace aina gina kamfanin shinkafar ne a Wushishi.
Tace shirin gina kamfanin yana karkashin hadaka ne da Gwamnatin jihar Naija ke yi da kamfanoni masu zaman kansu.
Wata matar aure dake aiki ta shiga tsaka mai wuya.
Tace a boye sunanta inda tace ta fara lalata da abokin aikinta a Ofis inda ya dirka mata ciki a karin farko.
Tace a lokacin dansu bai cika shekara guda ba, mijinta kuma yasha cikinsa ne dan haka yace ta zubar da cikin dan su samu su baiwa karamin dansu kulawa.
Tace saidai a karo na biyu, abokin aikin nata ya sake dirka mata ciki inda tace amma a wannan karin mijin nata yace kada ta zubar da cikin.
Musamman lura da cewa a baya ya sata ta zubar da cikin.
Tace abinda ke damunta shine mijin nata bai san cewa, cikin ba nasa bane gashi yana ta nan nan da ita.
shine take
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, an kai harin kunar bakin wake kusa da Abacha barracks inda aka yi sa'ar kashe dan kunar bakin waken.
Hoton da ba kyan gani ya nuna gawar maharin wanda aka kashe.
Rahotan yace karin mutum daya ya mutu.
Kalli Hoton anan
Wata Motar daukar Gawa ta yi kaca-kaca bayan da suka yi taho mu gama da wata motar dakon man fetur.
Motar dau na dauke da gawane yayin da hadarin ya faru.
Mafusata Sun Yi Silàr Mùtùwaŕ DPO'n 'Yañ Sanďà Na Garin Rano Bayan Sun Far Masa Sakamakon Zargiñsa Da Kàshè Wani Matashi Biyo Bayan Dukan Da Ya Yi Masa
Lamarin dai ya jawo konè-konè da fashè-fashen motocin 'yan sandan na garin Rano dake Kano, biyo bayan mutuwar matashin.
Majiyar Rariya ta tabbatar da cewa DPO'n ya rasa ne bayan gajeruwar jinya a asibiti.
Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya janye kudirin dokar da ke neman tilasta wa 'yan Najeriya kada kuri'a a kowane zaɓe.
Kudirin dai na neman gyara Dokar Zaɓe ta 2022, inda aka tanadi cewa duk masu cancantar kada kuri’a dole ne su fito su zaɓa a kowanne zabe, kuma wanda ya ki, zai iya fuskantar hukunci na daurin watanni shida zuwa tara, ko tara har Naira 100,000.
Sai dai, wannan kudiri ya jawo ce-ce-ku-ce daga jama’a da kungiyoyin kare hakkin dan adam. Kungiyar SERAP ta bayyana cewa wannan yunkuri ya sabawa yancin dan adam, kundin tsarin mulki da kuma dokokin kasa da kasa. Sun jaddada cewa 'yancin kada kuri’a yana nufin mutum na da damar yanke shawara – ya kada kuri’a ko kuma ya ki. Haka kuma, sun yi barazanar daukar matakin shari’a idan aka amince da kudirin.
Fi...