Sunday, April 5
Shadow
Nan da shekarar 2027 za’a samu karin Talakawa a Najeriya>>Inji Bankin Duniya

Nan da shekarar 2027 za’a samu karin Talakawa a Najeriya>>Inji Bankin Duniya

Duk Labarai
Bankin Duniya ya bayyana cewa talauci a Najeriya zai karu da kaso 3.6 a cikin 100 nan da shekaru 5 masu zuwa. Bankin Yace hakan zai farune duk da ci gaban da aka samu ta fannin tattakin Arziki. Bayan Najeriya akwai kuma kasashe irin su DR. Congo da suma ake tsammanin zasu fada cikin wannan matsanancin hali. Lamarin dai na zuwane a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara ta'azzara a tsakanin jihohin Arewa.
Ji yanda wani mutum kan zargin kàshè matar ƙaninsa a Jigawa

Ji yanda wani mutum kan zargin kàshè matar ƙaninsa a Jigawa

Duk Labarai
Rundunar ƴansanda a jihar Jigawa sun ce sun kama wani mutum bisa zargin kashe matar ƙaninsa a ƙauyen Gunka da ke karamar hukumar Jahun a jihar. Wata sanarwa da kakakin ƴansandan jihar SP Lawan Shiisu Adam ya fitar ranar Alhamis, ya ce ana zargin mutumin mai suna Buhari Sule mai shekara 25 da far wa matar ƙanin nasa - inda ya lakaɗa mata shegen duka har ta kai ga mutuwarta. Sai dai ya ce ana tunanin cewa ba shi da lafiyar kwakwalwa, saboda baya ga kashe matar, ya kuma raunata ɗiyar makwabciyarsa ta hanyar yi mata duka da taɓarya. Sanarwar ƴansandan ta ce lamarin ya faru ne ne ranar Laraba, 23 ga watan Afrilu da misalin karfe 5:30 na yamma a ƙauyen na Gunka. "Bayan da muka je wurin da lamarin ya faru ne muka garzaya da waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Jahun dom...
Sojojin Najeriya sun dakile yunkurin kai hàrì tare da kàshè ɗan bindiga a Filato

Sojojin Najeriya sun dakile yunkurin kai hàrì tare da kàshè ɗan bindiga a Filato

Duk Labarai
Rundunar sojin Najeriya ta Operation Safe Heaven ta ce ta daƙile wani yunkurin kai hari a ƙauyen Teegbe da ke karamar hukumar Bassa na jihar Filato, tare da kashe ɗaya daga cikin maharan. Sanarwar da mai magana da yawun rundunar Manjo Samson Nantip Zhakom ya fitar ranar Alhamis, ya ce lamarin ya faru ne ranar Laraba 23 ga watan Afrilu, inda artabun da sojojin suka yi da maharan ne ya janyo wasu suka tsere. "Wani mazaunin yankin ne ya kira mu ya faɗa mana abin da ke faruwa, daga nan dakarun mu suka garzaya wurin. Sun fafata da ƴan bindigar har ta kai ga kashe ɗaya daga cikinsu, tare da kama wasu mutum biyu waɗanda ake ci gaba da bincike a kansu," in ji Manjo Samson. Ya ƙara da cewa dakarun sun kuma samu nasarar kama wasu ƴan fashi uku a wani samame da suka kai hanyar Katnan- Burata...
Ma’aikatan Nimet sun janye yajin aiki

Ma’aikatan Nimet sun janye yajin aiki

Duk Labarai
Ƙungiyar ma'aikatan hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMET sun sanar da janye yajin aikin da suka fara ranar Laraba. Ma'aikatan sun ɗauki matakin janye yajin aikin ne bayan wata ganawa da suka yi da ministan sufurin ƙasar, Festus Keyamo a Abuja yau Alhamis. Yajin aikin da suka kira kan rashin ingantaccen albashi, ya haifar da cikas a filayen jiragen sama na cikin gida - inda fasinjoji da dama suka kasa yin balaguro. Ma'aikatan sun kuma ce sun damu matuka ganin cewa ba aiwatar musu da albashi mafi ƙanƙanta da gwamnatin tarayya ta amince da shi ba.
JARUMAR MATA: Tà Çàķawa Ķwàrtòn Da Ya Yi Yùnkùrin Yi Màťà Fýadè Wùķa A Garin Jòs

JARUMAR MATA: Tà Çàķawa Ķwàrtòn Da Ya Yi Yùnkùrin Yi Màťà Fýadè Wùķa A Garin Jòs

Duk Labarai
JARUMAR MATA: Tà Çàķawa Ķwàrtòn Da Ya Yi Yùnkùrin Yi Màťà Fýadè Wùķa A Garin Jòs. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Daga Aminu Lawal Hassan Wannan Halima Ibrahim 'ýa ta ce, mahaifinta Alh Ibrahim kanina (cousin) ne, su na zaune garin Jos. Shekaran jiya barawo ya shiga gidanta da rana ya yi ma ta sata sannan ya nemi ya yi ma ta fýaďè ta ki, shine ya sa wùķa ya nemi ya yi mata ýañķan rago Allah Ya tsare, amma ya ji ma ta çìwo a wuya, ita kuma cikin ikon Allah ta kwace wukar ta soke shi a ciki. Yanzu haka tana...
GWAMNATI ZA TA BA MAHAJJATA KUƊIN GUZIRINSU A HANNU

GWAMNATI ZA TA BA MAHAJJATA KUƊIN GUZIRINSU A HANNU

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki. Wata sanarwa daga ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ta ce shi ne ya nema wa mahajjatan sauƙin daga Babban Bankin Najeriya CBN. "An bayyana damuwa game da tsarin da CBN ya sharɗanta na kowane mahajjaci ya yi amfani da katin banki a matsayin wanda zai iya kawo tarnaƙi ga tsari da aikin gudanar da Hajjin 2025," in ji sanarwar da Stanley Nkwocha ya fitar. Ta ambato kwamashinan tsare-tsare da ayyukan kuɗi na hukumar alhazai, Aliu Abdulrazaq, na cewa hakan zai bai wa mahajjan Najeriya damar kashe da hannunsu yayin ibadar a Saudiyya. "Tun kafin yanzu mun sha yin ganawa game da kuɗin guziri a aikin Hajjin na 2025. Daga baya mataimakin shugab...
Haba shiyasa Hisbah suka Haramta jin wakar Hamisu Breaker, Kalli Bidiyon yanda Khadija Me Numfashi ta hau kan wakar take kwarkwasa kamar wata ‘yar India

Haba shiyasa Hisbah suka Haramta jin wakar Hamisu Breaker, Kalli Bidiyon yanda Khadija Me Numfashi ta hau kan wakar take kwarkwasa kamar wata ‘yar India

Duk Labarai
A safiyar yaune muka tashi da labarin cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta Haramta jin wakar Amanata ta Hamisu Breaker. Da yawa basu san wannan waka ba kamin Hisbah ta Haramtata, sai bayan da aka Haramtata ne mutane da yawa suka fara sauraren wakar. https://www.tiktok.com/@khadija_mainumfashi1/video/7496152812175281413?_t=ZM-8vnrbSyoDgs&_r=1 Bidiyon Khajida Me Numfashi data hau wakar tana bi ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ganta tana rawa da rausayawa kamar wata 'yar India. Mutane sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai sosai.
An bayyana abu daya da ya ragewa Atiku da Peter Obi su yi idan suna son kayar da Tinubu a zaben 2027

An bayyana abu daya da ya ragewa Atiku da Peter Obi su yi idan suna son kayar da Tinubu a zaben 2027

Duk Labarai
A yayin da komawar Kwankwaso jam'iyyar APC ke kara tabbata. Sannan mataimakin Atiku a zaben 2023, Ifeanyi Okowa shima ya koma APC. Sannan ake rade-radin shima mataimakin Peter Obi a zaben 2023, Datti Baba Ahmad wai zai koma APC, an bayyana abu daya da ya ragewa Peter Obi da Atiku Abubakar su yi shine su hade waje guda. Masu sharhi sun ce idan ba hadewa suka yi a waje guda ba, ba zasu iya kayar da shugaban kasa Bola Tinubu said a zaben 2027 ba.