Taya zan fara sana’a
Fara Sana'a abu ne me sauki sosai, musamman a wannan zamanin da muke na yanar gizo da kafafen sada zumunta.
A yanzu ba lallai sai kina ko kana da jari ba sannan zaka fara sana'a ba.
Kamin ka fara sana'a, yana da kyau kasan sana'ar kuma kasan ba a dare daya da fara wannan sana'a zaka yi nasara ba, akwai kalibale.
Yana da kyau amma ba lallai bane ya zama kana ko kina son sana'ar da kike, ko kake. Mana'ana, zai iya zama ka tsani sana'a amma tana kawo kudi, kaga kuwa bai kamata kawai dan ka tsaneta ka daina ba.
Ita sana'a yawanci yana da kyau a fara koyanta kamar yanda muka bayyana.
Kuma akwai hanyoyin koyo da yawa, wata kila tana bukatar ka je makaranta irin ta watanni 3 ko watanni shida dinnan wanda ake koya saka, dinki, da sauransu.
Ba lallai sai kin ko ka je irin wadannan...







