Ku Dai ku ci gaba da min fatan Alheri: Ni kuma ina bakin kokarina wajan Gyara kasarnan>>Shugaba Tinubu
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi kira ga 'yan Najeriya kada su yanke tsammani, su ci gaba da mai fatan Alheri game da ayyukan da yake yi.
Ya bayyana hakane a wajan taron jam'iyyar APC na kasa da ya gudana a fadarsa.
Yace yana fatan ganin karin 'yan Jam'iyyar Adawa suna shiga jami'iyyar ta APC.
Shugaban ya kuma gode da amincewar da aka bashi na shugabantar Najeriya.








