DA DUMI DUMI: Rahotanni Sun tabbatar da cewa Ganduje ya shiga ɗimuwa yakasa zaune yakasa tsaye Bisa jin cewar Kwankwaso Zai shiga cikin jam’iyyar Apc, An shiga fargaba a APC kan batun dawowar Kwankwaso jam’iyyar
Rahotanni Sun tabbatar da cewa Ganduje ya shiga ɗimuwa yakasa zaune yakasa tsaye Bisa jin cewar Kwankwaso Zai shiga cikin jam'iyyar Apc, An shiga fargaba a APC kan batun dawowar Kwankwaso jam'iyyar
A yayin da a ke ci gaba da rade-radin yiwuwar sauya shekar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso zuwa jam’iyyar mai mulki ta APC, wasu majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa wannan yunkuri na tsohon gwamnan jihar Kano ya haifar da fargaba a cikin jam’iyyar.
Majiyoyin jam’iyyar sun bayyana wa jaridar TRIBUNE cewa wannan yunkuri da ake cewa ya samo asali ne daga yarjejeniya tsakanin shugaban kasa Bola Tinubu da jagoran na NNPP, na janyo rashin jin dadi a bangaren shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Sanata Barau Jibrin, ...








