Sabuwar kungiyar dake ikirarin Jìhàdì me suna Làkùràwà ta karbe iko da kananan hukumomi 5 a jihar Sokoto
Sabuwar kungiyar dake ikirarin Jihadi me suna Lakurawa a jihar Sokoto ta karbe iko da wasu bangarori na kananan hukumomi 5 a jihar Sokoto inda take karbar Haraji da Zakka.
Kananan hukumomin da Kungiyar ta kama iko da su sun hada da Tangaza, Gada, Illela, Silame, da Binji kamar yanda wata majiya ta bayyanawa jaridar Vanguard.
Rahoton yace wannan kungiya ta Lakurawa na magana da yarukan Hausa, Fulani, Tuareg, Kanuri, Tuba, da Turanci.
Rahoton yace mutanen na zuwane a babura inda sukan bar wasu su musu gadi sannan su tafi wani garin.
Shugaban karamar hukumar Tangaza, Alhaji Isa Salihu Kalenjeni ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ko da kwanannan sai da suka kwacewa wani dan kasuwa Naira Miliyan 2 sannan suka kwace masa mota sai da ya biya Naira 350,000 sannan suka bar masa i...







