An zargi hukumar Yaki da rashawa da cin hanci, EFCC da zanewa wata budurwa mazaunai.
Lamarin ya farune dai bayan da EFCC suka kai samame a wani gidan rawa dake jihar Ondo.
Saidai zuwa yanzu hukumar ta EFCC bata ce komai ba kan wannan zargi da ake mata
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa shine gwarzon shugaban kasar da ya ajiye kwadayin sake cin zabe gefe guda, bai rufe masa ido ba, yayi abinda ya kamata na cire tallafin man fetur.
Ministan yada labarai, Muhammad Idris ne ya bayyana hakan a wani rubutu da yayi a wata jarida ta kasar Ingila.
Ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi abinda ya kamata na cire tallafin man fetur.
Sannan kuma shugaban ya cire tallafin dala da sauransu dan tayar da komadar tattalin arzikin Najeriya.
Cire tallafin man fetur din dai ya jefa 'yan Najeriya cikin halin matsin rayuwa, saidai Minista Muhammad Idris ya bayyana cewa, akwai matakai masu tsari da gwamnatin zata sake dauka nan gaba.
“The same has been the case with floating our currency, the Naira – a decision re...
Bidiyon wasu kananan yara 'yan mata dake tsakanin shekaru 15 zuwa 16 su 10 da aka dauka daga Najeriya aka kaisu kasar Ghana yin karuwanci ya tayar da hankula.
Bidiyon ya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda aka gansu ana tambayarsu kowace na fadin shekarunta da jihar data fito, yawancinsu sun fito ne daga jihar Imo kuma daga cikinsu akwai guda 3 wanda uwarsu daya ubansu daya.
https://twitter.com/Onsogbu/status/1799027863666262141?t=kBSG-jgJbFcfH_XL3BV3Rw&s=19
Ko da aka tambayesu iyayensu sun san sun tafi karuwanci? Sai suka ce a'a.
Lamarin dai ya dagawa mutane hankula sosai inda akai ta musu Allah wadai.
Tuni dai gwamnatin tarayya ta sanar da fara bincike kan lamarin.
Ama kan hakane Gwamnatin ta yi sabuwar dokar da ta hana zuwan kananan 'yan mata da basu ci...
Gwamnatin tarayya karkashin Ma'aikatar mata ta haramtawa Kananan yara 'yan kasa da shekaru 18 shiga otal.
Ministar matan, Uju Ohaneye ce ta bayyana hakan inda tace dole duka otal din dake Najeriya dolene su bi wannan umarni.
Tace duk Otal din da aka samu bai bi wannan umarni ba zai iya fuskantar hukuncin dakatarwa.
Tace an dauki matakanne dan kawar da matsalar safarar 'yan mata.
Hakan na zuwane dai a yayin da wasu bidiyon 'yan mata dake da shekarun tsakanin 15 zuwa 16 aka ga an yi safarar su zuwa kasar Ghana dan yin Karuwanci.
Babban malamin addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami kenan a wadannan hotunan tare da malamai abokansa.
https://twitter.com/ProfIsaPantami/status/1799702225411043418?t=R6pngDgWCiYXtOoWkuIqDA&s=19
Sheikh Pantami ya wallafa hotunan a shafinsa na sada zumunta inda masoyansa da yawa suka yaba
Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima.
DAGA: Abbas Yakubu Yaura
Wani jigo a jam’iyyar, NNPP, Buba Galadima ya ce ba zai taba yiwuwa ɗaukacin yankin Arewa su samu ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya a zaɓen 2027 ba.
A wata hira da jaridar Sun, tsohon sakataren rusasshiyar jam'iyyar CPC, ya bayyana cewa a tsarin dimokuradiyya irin na Najeriya, masu zaɓe na da ƴancin yin zaɓi daban-daban.
Da aka tambaye shi ko ƴan Arewa za su zaɓi Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, ko kuma takwaransa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, Galadima ya ce, “Ba ma cikin còci; Ba ma cikin másallaci. Me ya sa za mu yi magana da murya ɗaya?
“Dimokradiyya kenan."Idan ka haɗa mutane uku tare, kowa ya sami hanyar t...
Madugun Kwankwasiyya kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya zargi 'yan adawa a Kano da cin dunduniyar gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf har tsawon shekara guda.
Kwankwaso ya fadi haka ne a lokacin da gwamnatin Kano ta ayyana dokar ta-baci kan ilimi a jihar Kano a yau Asabar.
Ya ce, “Bari in fara da taya shi murnar wannan rana mai cike da tarihi, ranar da gwamna ke ayyana dokar ta-baci kan ilimi. Sanin kowa ne cewa gwamna yana aiki tun daga ranar da ya hau mulki a ko’ina a fadin jihar.
“Duk da cewa gwamnan ya na fuskantar kalubale tsawon shekara guda. Nan da nan bayan zaɓe, maƙiyan Jiha sun kai shi Kotu, zuwa Kotun Daukaka Kara zuwa Kotun Koli. Mun ga abin da ya faru duk da sun san cewa babu bukatar a je wata Kotu. Kowa ya san cewa ya ci zabensa...
Iya Yawan Yin "Mining" Ɗinka, Iya Talaucinka, Inji Naziru Sarkin Waƙa
Maganar Mawaƙin na cigaba da jawo cece-kuce da kuma zazzafar muhawara musamman a tsakanin matasa.
Ko me.za ku ce akan wannan magana ta Sarkin Waƙa?
Daga Abubakar Shehu Dokoki
TIRKASHI: Ya Saki Matarsa Saboda Ganyen Shayi, Bayan Tsawon Shakara Goma Suna Zaman Aure
Daga Mubarak Ibrahim Lawan
"Da Asubahi ta gaya wa mijin cewa ganyan shayi ya ƙare. Wajen ƙarfe shida na safe kuma ƙaninsa ya zo ya ɗauke shi suka tafi jana'izar wani abokin kasuwancinsu. Bayan ya dawo gida wajen ƙarfe 9 na safiyar, sai ya tarar yaransa ba su tafi makaranta ba. Ya tambayi dalili sai ta ce ai bai kawo ganyen shayin da za su yi karin kumallo ba. Daga nan fitina ta fara. A yinin ya sallame ta.
Lokacin da iyaye suka shiga maganar, sai ya ce ya gaji da zama da macen da ta ke kasa yi masa hidimar naira 100 duk da cewa shi ya na iya yi mata hidimar miliyan 5 domin, a shekarar bara ma ya kai ta Hajji, ya canja mata kujeru, kuma ya tabbatar cewa shi ya sama mata aikin da ta ke yi. Ya ƙa...