Tapswap, Notcoin: Hatsarin shafukan kirifto da ‘yan Najeriya suka ruɗu da su
Tun bayan fashewar Notcoins, matasa a Najeriya suka mayar da hankalai wajen yin mainin, domin tara maki ko 'points' a cikin manhajojin da suke amfani da su a wayoyinsu.
Daga lokacin ne kuma harkar kirifto ke ƙara samun karɓuwa a Najeriya, inda a kowace rana ake samun ƙaruwar ɓullar sabbin shafukan mainin da ke alƙawarta samar wa mutane kuɗi.
Masu amfani da shafukan ko manhajojin kan yi ta taɓa sikirin ɗin wayarsu domin samun wani maki da ake kira 'points', wanda za a iya canjawa zuwa kuɗi ''idan ta fashe''.
A yanzu akwai sabbin manhajojin waya da dama da ake amfani da su domin samun kuɗin.
Fitattu daga ciki sun haɗa da Notcoins da Tapswap da Hamstar Kombat da Poppo da sauransu.
Yayin da wasu mutane ke darawa saboda kuɗin da suka ce sun samu sakamakon fashewar Notcoins, wasu ...








