Saturday, December 20
Shadow
Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa

Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa

Siyasa, Tarihi
Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa. A ranar 8 ga watan Yuni 1998 Allah Ya yi wa tsohan shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja, Janar Sani Abacha rasuwa; Yau shekara ashirin da shidda da ke nan. Da Wadanne Irin Ayyukan Alheri Ku Ke Tunawa Da Shi? Allah Ya Jikansa Da Rahama! Daga Jamilu Dabawa
Real Madrid ta fi kowace kungiya kyau a Duniya>>Inji Messi

Real Madrid ta fi kowace kungiya kyau a Duniya>>Inji Messi

Kwallon Kafa, labaran messi na yau, Wasanni
Tauraron dan kwallon MLS kuma tsohon dan wasan Barcelona, Lionel Messi ya bayyana cewa, Kungiyar Real Madrid ta fi kowace kungiya Kyau a Duniya. Ya bayyana hakane yayin hirar da aka yi dashi da wata kafa me suna Infobae. Ya bayyana cewa idan sakamako me kyau ake magana, Real Madrid ce kungiyar data fi kowace amma idan kuma iya wasane, ya fi son Guardiola inda yace duk kungiyar da Guardiola ya horas zaka ganda ta yi fice. Yace dan haka iya wasa sai Manchester City amma kuma sakamako sai Real Madrid. Kuma wannan ra'ayi na Messi bai zo da mamaki ba ganin cewa, Real Madrid ce ta lashe kofin zakarun nahiyar turai.
Dole a samar da inshola ga masu haƙar ma’adanai – Gwamnatin Najeriya

Dole a samar da inshola ga masu haƙar ma’adanai – Gwamnatin Najeriya

Siyasa
Gwamnatin Najeriya ta tilastawa kamfanonin haƙar ma'adanai yin inshola ga ma'aikatan su, domin bayar kariya gare su idan wani haɗari ya faru. Ministan ma'adanan ƙasar, Dele Alake, ya daga yanzu gwamnati ba za ta sake amincewa da lasisin duk wani kamfanin haƙar ma’adanai da bai nuna ƙwaƙwarar shaidar cika ƙa'idojin gudanar da aiki ba. Ministan ya na magana ne lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya da jaje a jihar Neja, inda ƙasa ta rufta da masu haƙar ma'adanai a ƙauyen Galkogo na ƙaramar hukumar Shiroro. Ya ce gwamnati za ta tabbatar da bin duk hanyar da ta dace domin kare afkuwar irin wannan matsala a nan gaba, dmin haka ta faraɓullo da irin wannan mataki. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja a Najeriya (NSEMA) ta ce kimanin mutum 30 ne ake fargabar sun mutu sakamakon za...

Me ake karantawa a sallar gawa

Ilimi
Ga abinda ake karantawa a Sallar Gawa kamar haka: Bayan kabbarar farko ana karanta Fatiha. Bayan Kabbara ta biyu ana karanta Salatin Annabi(SAW). Bayan kabbara ta uku sai a yiwa mamaci addu'a. Bayan kabbara ta hudu sai mutum yawa kansa addu'a. Shikenan kuma sallama daya ake yi.
Me ake nufi da aure

Me ake nufi da aure

Auratayya
Aure wata tarayya ce ko zama tsakanin namiji da mace wadda Addini da Al'ada sun mince dashi. Ana aure ne tsakanin Namiji da mace wanda suka amince su zauna tare su gina iyali da samun zuri'a. A musulunci, Aure sunnar Annabi Muhammad(Sallallahu Alaihi Wasallam) ne. Hanyar aure itace mafi tsafta ta samun zuri'a da cikar mutunci da nasaba. Duk wanda aka sameshi ta hanyar aure to zaka ga murna ake dashi, ba'a tsangwamarshi ba'a yi masa gori, saboda yana da uwa da uba. Shi kuwa wanda aka samu ba ta hanyar aure ba, duk da ba laifin shi bane zaka ji ana ce masa shege da gorin Uba da sauransu.

Me ake nufi da wasa kwakwalwa

Ilimi
Wasa Kwakwalwa na nufin yin wani da zai sa ka yi tunani ko nazari wajan samar dashi. Ko kuma ka yi Tunani ko Nazari wajan warware wata matsala, hakan na iya zama a makaranta ko kuma a rayuwarka ta zahiri. Misalin Wasa kwakwalwa shine idan aka tambayeka jihohi Nawane a Najeriya?, Ko ace maka goma a tara da takwas a debe uku. Ko kuma ace maka idan aka hada ruwa da madara da zuma me zasu bayar? Ko ace maka baba na daka gemi na waje, watau Hayaki, ko ace maka ja ya fado ja ya dauka, watau dan fulani da kayan giginya. Da dai sauran su.
Me ake nufi da naso a hausa

Me ake nufi da naso a hausa

Ilimi
Naso na nufin likewar wani abu a jikin wani abu ko kuma bayyanar wani abu a jikin wani abu dalilin haduwarsa da wani Abu. Misali, idan ka zuba ruwan sanyi a cikin kofi, zai yi naso a jikin kofin ta baya inda zaka rika ganin kamar zufa a bayan kofin. Ko kuma idan ka samu rigar bakanike, zaka ga bakin mai ya manne a jikinta, wannan mannewar ita ake kira da Naso. Ko kuma idan gini yana kusa da ruwa, zaka ga kasan katangar ginin kamar ta jike, wannan ma naso ne. Ina fatan wadannan misalai dana baka sun sa ka fahimci ko kin fahimci me ake nufi da Naso a Hausa.
Ina ake buga kudin nigeria

Ina ake buga kudin nigeria

Kasuwanci, Tarihi
Kanfanin Nigerian Security Printing and Minting (NSPM) ne ke buga kudin Najeriya. Kuma kamfanin na zaunene a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. A baya dai akan kai Kwangilar buga kudin zuwa kasashen waje amma a zamanin Mulkin Shugaba Buhari, an buga kudin na Naira a Najeriya. Saidai a duk sanda aka buga sabbin kudi, 'yan Najeriya kan yaba inda wasu ke kalubalantarsu, musamman ma dai ta bangaren ingancin Kudin.
Majalisar Dinkin Duniya ta saka Kasar Israela cikin masu kisan kananan yara

Majalisar Dinkin Duniya ta saka Kasar Israela cikin masu kisan kananan yara

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Siyasa, Yakin gaza da isra'ila
Majalisar Dinkin Duniya ta saka kasar Israela cikin kasashe masu kisan kananan yara. Hakan ya biyo bayan kisan sa kasar kewa Falas-dinawa a zirin gaza. Wakilin Israela a Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan ne ya bayyana haka. Inda yace an sanar dashi matakinne ranar Juma'a. Hakanan ministan harkokin kasashen waje na kasar Israela, Katz ya bayyana cewa, zasu dauki mataki kuma wannan abu da majalisar ta yi zai canja dangantakar dake tsakaninsu da Israela.
Kalli Hoto: Sabuwar cuta dake yaduwa ta hanyar Jima’i ta bayyana

Kalli Hoto: Sabuwar cuta dake yaduwa ta hanyar Jima’i ta bayyana

Kiwon Lafiya
Wata cuta da aka kira da Ring worms dake yaduwa ta hanyar Jima'i ta bayyana. Cutar dai wadda irintace a karin farko da aka gani a jikin dan adam ta bayyana ne a jikin wani dan kasar Amurka. Mutumin dai dan Luwadi ne wanda kuma yaje kasashe daban-daban yayi lalata da maza masu yawa. Bayan da ya koma kasarsa ta Amurka ne sai aka ganshi da wannan cuta. Saidai masana kimiyyar lafiya sun ce kada mutane su tayar da hankali dan cutar bata kai matakin barazana ga sauran al'umma ba. Ko da dai cutar Kanjamau akwai wasu majiyoyi dake cewa daga wajan 'yan Luwadi aka fara samota, hakanan ta tabbata cewa masu Luwadi sun fi saurin kamuwa da cutar.