Wannan bawan Allahn 'yan Bindiga sun kasheshine a jiya, Alhamis.
Dansa ne ya wallafa hakan a shafinsa na sada zumunta inda yace:
Kulli nafsin za ikatul mautAllah yayi ma yayan mahaifina rasuwa wanda aka sani daAlhaji babangiga wanda yan ta adda suka kashe a jiya alhamis
Tsohon ministan matasa da wasanni, Barista Solomon Dalung ya ce shi a fahimtarsa Najeriya ba ta kai mizanin da ake so ba dangane da romon dimokraɗiyya.
"A shekara 25 ɗin nan a gare ni ba ta haifi ɗa mai do ba....An sami komabaya a tattalin arziki na Najeriya domin a 1999 lokacin da aka kawo wannan dimokraɗiyya, canjin dala a lokacin yana ƙasa da naira 10 amma a yau muna maganar kusan naira 1500." In ji tsohon ministan.
Dangane da ilimi, Dalung ya ce "ba ma za ka taba haɗa ingancin ilimi na wancan lokacin da na yanzu ba."
Harkar noma da kiwo da zamantakewa da tsohon ministan ya yi magana a kai, ya ce duka komabaya aka samu.
Da aka tambaye shi ko daga wane lokaci al'amura suka taɓarɓare kasancewar shi ma ya kasance a wata gwamnati a baya. Sai ya ce " tsarin ne ba mai kyau ba. Ida...
Nan gaba a yau, Juma'a ne wata babbar kotun tarayya za ta saurari ƙarar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya shigar gabanta, inda yake neman kotun ta hana kama shi, sannan kuma a mayar da shi gidan sarki na ƙofar kudu.
Cikin waɗanda sarkin ya shigar da su ƙarar har da ƴansanda da jami'an tsaro na civil defence.
Ranar 28 ga watan Mayu mai shari'a Amobeda Simon ya bayar da umarnin cewa waɗanda ake ƙarar kada wanda ya hana shi shiga gidan sarki na kofar kudu ko hana shi amfani da duk wasu abubuwan da ya cancanta a matsayin sarki.
Sannan umarnin kotun ya ce kada fitar da duk wanda yake cikin gidan sarki ba bisa ka'ida ba, har zuwa lokacin da kotun za ta saurari buƙatar da aka gabatar mata.
A yau ne kuma kotun za ta zauna don sauraren ƙorafin da Sarkin, na 15 na Kano ya shigar.
...
An daura auren tsohuwar Jarumar Kannywood kuma tsohuwar matar Sani Musa Danja, Mansura Isah a yau Alhamis, kamar yadda ƙawarta Samira Ahmad ta wallafa a shafinta na Instagram.
Sai dai Samirar ba ta bayyana sunan mijin da Mansura Isah ta aura ba.
Allah ya tabbatar da Alkairi
Rahotanni daga Bassa da Erena a jihar Naija na cewa mayakan kungiyar B0k0 Hqrqm sun kai mummunan hari a yankin.
Majiyar Hutudole tace an kai harinne a garin Makuba Lantan Bakin Kogi Bassa inda aka kashe mutane 7 ta hanyar yi musu yankan rago.
Harin ya farune a jiya, Alhamis kamar yanda majiyar tamu ta tabbatar.
Masu fada a ji a yankin sun nemi mahukunta da su kaiwa mutanen yankin musamman wadanda suka rasa muhallansu dauki.
Mun samu hoton kan daya daga cikin mutanen da aka yanke, Allah ya kyauta.
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, matakan tada komadar tattalin arziki da zata dauka nan gaba, sai sun fi na baya tsanani.
Hakan na fitowane daga bakin Ministan yada labarai, Muhammad Idris.
Ya kara da cewa daukar wadannan matakai ya zama dole dan canja fasalin Najeriya ta yanda zata ci gaba ta fannin tattalin arziki.
Ya bayyana hakane a wani rahoto da aka wallafa a wata jaridar kasar Ingila.
Minista Muhammad Idris ya kara da cewa, Shugaba Tinubu gwarzo ne dan kuwa ya dauki matakan da shuwagabannin da suka gabata, suka kasa daukar irinsu.
Babban matakin da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta dauka wanda ya damu al'ummar kasar shine cire tallafin man fetur wanda ya yi sanadiyyar jefa mutane cikin halin kaka nikayi.
Hakanan gwamnatin Tinubun ta kuma cir...
Gwamnan jihar Rivers, Sim Fubara ya baiwa mahajjatan jiharsa kyautar dala $300.
Ya bukata mahajjatan da su zama wakilan jihar da kuma Najeriya na gari a kasa me.tsarki, kada su yi abinda zai bata sunan jihar ko Najeriya.
Ya kuma bakaci mahajjatan da su saka Najeriya a addu'a a yayin ibadarsu a kasa me tsarki.
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Maryam Yahya kenan a wannan hoton inda take a birnin Yiwu na kasar China.
Ta saka hoton ne a shafinta na sada zumunta inda masoyanta da dama suka yaba.
Rahotannin da muke samu na cewa, fadar shugaban kasa ta musanta wasu bayanai dake cewa ministan kudi ya gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Naira Dubu dari da biyar(105,000) a matsayin mafi karancin Albashi.
Babban me baiwa shugaban kasa Shawara kan harkar yada labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka ta shafinsa na sada zumunta.
Ga sakonsa kamar haka:
"The Honorable Minister of Finance and coordinating minister of the economy, Wale Edun has not proposed N105,000 minimum wage. The contrary story being disseminated is false.”