Zanga-zanga ta barke a Kano kan rikicin sarautar da ya faru a jihar.
An ga wasu matasa dauke da kwalaye inda suke ihun basa so.
An kuma ga an kunnawa taya wuta a karkashin wata fastar Abba da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
https://twitter.com/daily_trust/status/1794756398351356238?t=lWt28qaBdF9DMh57LPzSgw&s=19
Daily Trust ta wallafa bidiyon wanda ya nuna abinda ke faruwa.
A wani bidiyon kuma an ga matasan na kabbara:
Jaridar dai tace matasan dake zanga-zanga suna neman a sake dawo da Sarki, Aminu Ado Bayero ne kan karagar Mulkin Kano:
https://twitter.com/daily_trust/status/1794760364070187113?t=-yPmQeNl8DbliJ5gkTzO7Q&s=19
Lamari dai ya kazancene bayan da Aminu Ado Bayero ya dawo Kano kuma ya sauka a gidan sarki dake Nasarawa.
Dan wasan Manchester United Kobbie Mainoo kenan a wannan hoton inda kafarsa ta dauki hankula a shafukan sada zumunta.
An dai ga kafar tasa kamar ta me yawo a kafa:
Diyar marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Sani Abacha, Gumsu Sani Abacha, ta saka hoto a shafinta na sada zumunta babu dankwali.
Wani ya jawo hankalinta da cewa, ta saka dankwali, saidai tace masa ya yi harkar gabansa.
Wadannan Daraktocine da babban bankin Najeriya, CBN ya kora daga aiki su 14.
A kwanannan ne dai aka samu rahoton cewa, CBN din ta kori ma'aikata 200 da suka hada da manya da kanana.
Clement Oluranti Buari, Director, Strategy Management
Dr Blaise Ijebor, Director, Risk Management
Lydia Ifeanyichukwu Alfa, Director, Internal Audit
Jimoh Musa Itopa, Director, Capacity Development
Muhammad Abba, Director, Human Resources
Rabiu Musa, Director, Finance
Dr Mahmud Hassan, Director, Trade & Exchange
Dr Ozoemena S. Nnaji, Director, Statistics
Dr Omolara Duke, Director, Financial Markets
Chibuike D. Nwaegerue, Director, Other Financial Institutions Supervision
Chibuzo A. Efobi, Director, Payments System Management
Haruna Bala Mustafa, Director, Financial Pol...
Mataimakin Peter Obi a takarar shugabancin Najeriya da suka yi a shekarar 2023, Datti Baba Ahmad ya bayyana cewa ba zai daina fada ba cewa, Peter Obi ne ya lashe zaben shekarar 2023.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.
Yace a lokacin da ake aikawa da sakamakon zabe ga hukumar INEC an kulle dadamalin yanar gizo da ake aikewa da sakon.
Yace aka koma karbar sakon da hannu inda aka juya lamura. Ya kuma kara da cewa jam'iyyarsu a yanzu ta fi jam'iyyar CPC a zaben 2013/2014 karfi nesa ba kusa ba.
Ya kara da cewa, tattalin arzikin Najeriya sai kara durkushewa yake, sannan kuma akwai cin hanci da rashawa sosai.
Jirgin kasan dake zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna yayi hadari a yau, Lahadi.
Jirgin yayi hadarin ne a daidai Jere.
Jirgin ya tashi ne daga Kaduna zuwa Abuja da misalin karfe 8:05 na safiyar ranar Lahadi.
Kuma ya sauka daga kan titinsa a daidai garin Jere.
Jami'an tsaron sojoji dana 'yansanda sun je wajan da hadarin ya faru.
Hukumar NIBS ta sanar da cewa tana sane da faruwar lamarin kuma ta tura jami'anta zuwa wajan.
Me martaba Sarki Muhammad Sanusi II ya bayyanawa jami'an tsaro cewa abinda Gwamnatin jihar Kano ta yi na sauke Aminu Ado Bayero ta mayar dashi kan kujerar sarautar Kano, Adalci ne.
Ya bayyana hakane a wani zama da suka yi shi da shuwagabannin jami'an tsaro na Sojoji, DSS, da 'yansanda.
Jami'an tsaron sun bayyanawa sarkin cewa, akwai dokar data ce a dakatar da mayar dashi akan kujerar sarautar Kano.
Saidai ya bayyana musu cewa, shi bai san da hakan ba, bai ma san da zaman kotun ba, kotun yanar gizo ce.
A lokacin da ya karbi takardar sake nadashi sarautar Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa, dama a baya ya fada, Allah ne me bayar da mulki kuma ya karba a lokacin da ya so.