Thursday, March 5
Shadow
Da Duminsa: Babbar Kotu a Abuja ta Haramta Zàngà-zàngà

Da Duminsa: Babbar Kotu a Abuja ta Haramta Zàngà-zàngà

Duk Labarai
Wata babbar kotu dake babban birnin tarayya, Abuja ta haramta yin zanga-zanga. Kotun tace ba'a amince wani dan zanga-zanga ya hau kan titin babban birnin tarayya Abuja ba da sunan zai yi Zàngà-zàngà. Ministan Abuja, Nyesome Wike ne ya gabatar da wannan korafi a gaban kotun. A baya dai masu zanga-zangar sun nemi a basu filin Eagle Square dan amfani dashi wajan gudanar da gangaminsu amma hukumomi suka kiya. A yanzu masu zanga-zangar sun bayyana cewa ko an yadda ko ba'a yarda ba zasu yi amfani da filin.
Ana harbi ko aka kàshe mutum daya zamu ajiye duk wasu bukatu zamu koma neman sai Tinubu ya sauka daga mulki>>Inji Masu Zàngà-zàngà

Ana harbi ko aka kàshe mutum daya zamu ajiye duk wasu bukatu zamu koma neman sai Tinubu ya sauka daga mulki>>Inji Masu Zàngà-zàngà

Tsaro
Matasa masu shirin fita Zàngà-zàngàr tsadar rayuwa sun gargadi hukumomi kan cewa kada a sake a harbi ko a kashe ko da mutum daya a cikinsu. Sunce muddin aka yi hakan, to lallai zasu ajiye duk wasu bukatunsu su koma neman sai Bola Ahmad Tinubu ya sauka daga mulki. Daya daga cikin wakilan kungiyar, Damilare Adenola ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Ya kara da cewa ba zasu bari jinin 'yan uwansu ya zuba a banza ba.
Sheikh Alkashnawy Ya Kammala Karatun Digirinsa Na Biyu Da Sakamako Mafi Daraja A Jami’ar Annadha Dake Ƙasar Niger

Sheikh Alkashnawy Ya Kammala Karatun Digirinsa Na Biyu Da Sakamako Mafi Daraja A Jami’ar Annadha Dake Ƙasar Niger

Duk Labarai
Daga Comr Nura Siniya Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya daga jihar Katsina Sheikh. Mal. Ismail Zakariya Alkashnawy, ya kammala karatun sa na digirin digirgir (PhD) a ɓangaren Larabci a jami'ar Annahdha International University da ke Niamey a ƙasar Niger. Haziƙin Malamin Dr. Alkashnawy, ya nuna hazaƙa sosai, yayin da ya kammala karatun da mataki mafi daraja (First Class).
Hukumar ‘yansanda tace duk wani dansanda dake hutu ya koma bakin aiki saboda zàngà-zàngàr gobe kuma kada dansandan daya sha giya dan kada yayi tambele a wajan Zàngà-zàngàr

Hukumar ‘yansanda tace duk wani dansanda dake hutu ya koma bakin aiki saboda zàngà-zàngàr gobe kuma kada dansandan daya sha giya dan kada yayi tambele a wajan Zàngà-zàngàr

Tsaro
Hukumar 'yansandan Najeriya ta bayyana cewa, duk wani dansanda dake hutu ya koma bakin aiki. Wannan mataki na zuwane yayin da ake kusa da fara Zàngà-zàngàr kukan tsadar rayuwa a Najeriya. Hakanan sanarwar ta bayyana cewa, kada a sake a samu wani dansanda da shan giya dan kada yayi tambele a wajan zanga-zangar. Hakanan an bukaci duka 'yansanda dasu saka kayan aiki cikakku a goben kuma an dakatar da kowane irin hutu.
Darajar Naira ta kara faduwa a kasuwar Chanji inda aka sayi dala akan Naira 1,575

Darajar Naira ta kara faduwa a kasuwar Chanji inda aka sayi dala akan Naira 1,575

Nawa ne farashin dala a yau
Darajar Naira ta kara faduwa a kasuwar bayan fage ta 'yan Chanji indaka sayi dalar Amurka akan Naira 1,575 a ranar Laraba. A ranar Talata dai an sayi dalar ne akan Naira 1,565. Hakanan a kasuwar gwamnati ma Darajar Nairar kara kasa ta yi inda aka sayi dala akan Naira 1,586.71. Hauhawar farashin dala dai na daya daga cikin abubuwan da ake alakantawa da hauhawar farashin kayan masarufi. Musamman lura da cewa mafi yawan kayan amfani aana shigo dasu Najeriya ne daga kasashen waje.
Tonon Silili, Kalli Hotuna: An Bayyana ‘yan matan kakakin majalisar tarayya, Godswill Akpabio har su 5

Tonon Silili, Kalli Hotuna: An Bayyana ‘yan matan kakakin majalisar tarayya, Godswill Akpabio har su 5

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Rahotanni sun bayyana cewa, kakakin majalisar tarayya, Godswill Akpabio wanda shine mutum mafi matsayi na 3 a Najeriya yana da tarin 'yan mata da yawa. Kafar GistLover ce ta yi wannan tonon Silili inda ta wallafa hotunan 'yan matan da ake zargin na kakakin majalisar ne. Daga cikin 'yan matan da ake zargin Godswill Akpabio da yin lalata dasu hadda shahararriyar me girkinnan ta Najeriya, Watau Hilda Bachi da Nancu Isime da Dakore Egbuson-Akande da dai sauransu. Saidai Tun...
Tunda an gaya shuwagabanni Allah sun ki ji, To  a fito a musu zàngà-zàngà kawai>>Inji Alhaji Haruna Sharu

Tunda an gaya shuwagabanni Allah sun ki ji, To a fito a musu zàngà-zàngà kawai>>Inji Alhaji Haruna Sharu

Duk Labarai
Alhaji Haruna Sharu, wanda shine shugaban rukunin gidajen Sharu ya bayyana cewa tunda shuwagabanni sun ki jin wa'azin da ake musu, mafita data rage itace a fito a musu zanga-zangar. Ya bayyana hakane a yayin da aka tambayeshi ra'ayinshi kan zanga-zangar sa ake shirin yiwa shuwagabanni a Arewa. https://twitter.com/shehu_mahdi/status/1815514836064690631?t=m38fOJAdFs0olHjIa1da9g&s=19 Ra'ayoyi sun banbanta kan yi ko jinkirta Zanga-zangar da matasa suka shirya kan taadar rayuwa.