Saturday, December 20
Shadow
Saida muka gargadi Wike kada ya je waja da Soja Yerima yake amma yakiya, Dan haka abinda sojan yayi abin yabawa ne>>Inji Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle

Saida muka gargadi Wike kada ya je waja da Soja Yerima yake amma yakiya, Dan haka abinda sojan yayi abin yabawa ne>>Inji Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle

Duk Labarai
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa, sai da suka gargadi Wike kada ya je ya fuskanci sojan ruwa, A. Yerima ya bari sojoji su kammala bincikensu akan filin amma yaki ya. Yace abinda sojan yayi ya aikata daidai bai aikata laifi ba domin yana bin umarnin na sama dashi ne. Yace kuma jami'an gwamnati su guji wulakanta sojoji dan yin hakan kamar wulakanta shugaban kasa ne. Yace Wike bai kamata ace yayi ja in ja da matashin sojan ba, kamata yayi ace ya nemi manyan sojan yayi magana dasu. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a DCL Hausa.
Kalli Bidiyo: A gidana kowa abinci kala daya yake ci, Tun daga Megadi, Direba har ni duk kalar abincin dana ci shi zasu ci>>Inji Shahararren Mawakin, Davido

Kalli Bidiyo: A gidana kowa abinci kala daya yake ci, Tun daga Megadi, Direba har ni duk kalar abincin dana ci shi zasu ci>>Inji Shahararren Mawakin, Davido

Duk Labarai
Shahararren Mawakin Najeriya, Davido ya bayyana cewa duk kalar abincin daya ci, shine Direbansa da kowa da kowa yake ci a gidansa. Ya bayyana cewa, matarsa na tabbatar da hakan inda yace irin tarbiyyar da aka masa a gidansu kenan. Davido wanda mahaifinsa shahararren me kudine yace a baya babu wanda yasan mahaifinsa duk da yana da kudi amma da ya fara wakane ya rika fadin irin abinda mahaifinsa ya mallaka mutane suka fara sanin wanene mahaifinsa. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. https://www.tiktok.com/@boyjulian.22/video/7571427066902564152?_t=ZS-91MTYhXyKzg&_r=1
Da Duminsa: Gwamnati tasa a yi abincike kan takaddamar data faru tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da soja A. Yerina

Da Duminsa: Gwamnati tasa a yi abincike kan takaddamar data faru tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da soja A. Yerina

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Ministan Tsaro, Muhammad Badaru yasa a gudanar da bincike kan takaddamar data faru tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da sojan Ruwa, A. Yerima. Saidai Ministan yace zasu tabbatar duk sojan dake bakim aikinshi yayi aikinshi da kyau an bashi goyon baya da kariya. Ya jinjinawa soja Yerima bisa kwarewar aiki da ya nuna a yayin takaddamarsa da Nyesom Wike.
Najeriya zata fita daga talaucin da tae fama dashi>>Inji Shugaba Tinubu

Najeriya zata fita daga talaucin da tae fama dashi>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da tabbacin cewa, Najeriya zata fita daga Talaucin da take fama dashi. Ya bayyana hakane ranar Laraba a wajan taron kungiyar mawallafa jaridu ta Najeriya. Yace lallai Najeriya na fama da talauci amma kuma ba zata kasance cikin Talauci ba nan da shekaru masu zuwa. Shugaban ya bayyana cewa, Gyare-Gyaren da ya dauko suna da tsauri da wahala amma ya daukosu ne da gyaran Tattalin Arzikin Najeriya.
Filaye Hectares 30 ne Wike ya kwacewa sojoji a Abuja, Ji karin bayani

Filaye Hectares 30 ne Wike ya kwacewa sojoji a Abuja, Ji karin bayani

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Filaye Hectares 30 ne aka baiwa manyan sojoji masu ci da wadanda suka yi Ritaya ministan babban birnin tarayya, Abuje Nyesom Wike ya kwace. Rahoton Sahara reporters yace Wike bayan kwace filayen ya rabawa abokai da na kusa dashi su . Saidai filin da suka yi rikici da Soja Yerima akai, Wike yayi rikici da soja me filin inda suka ce masa ya je kotu kamar yanda yakan gayawa mutane idan ya kwace musu fili. Amma saboda yasan bashi da gaskiya, Bai je kotun ba. Shine ya kwashi jami'an tsaro kusan 50 da motocin rushe gini ya nufi filin dan kwace shi amma ya hadu da Turjiya daga wajan soja Yerima.
Da Duminsa: Bayan Rikicin Wike da Sojan Ruwa, shugaba Tinubu yace Sojoji sun cancanchi yabo

Da Duminsa: Bayan Rikicin Wike da Sojan Ruwa, shugaba Tinubu yace Sojoji sun cancanchi yabo

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa kokarin sojojin Najeriya da suke sadaukar da rayuwarsu da sauran 'yan Najeriya su samu tsaro. Shugaban ya bayyana hakane a wajan taron kungiyar Mawallafa jaridu ta kasa Yace lallai Najeriya na fuskantar Kalubalen tsaro. Sannan ya jadada goyon bayan sojojin da ke sadaukar da rayuwarsu dan samar da tsaron.
Kalli Bidiyo: Ana rade-radin AhmadXM zai kara aure da kawar matarsa Safeera me suna Raihana

Kalli Bidiyo: Ana rade-radin AhmadXM zai kara aure da kawar matarsa Safeera me suna Raihana

Duk Labarai
Hattara matan Aure masu close friends ko bestie dabasuyi aureba, Naleko nakawo muku gulma Dake faruwa a TikTok, Rihanna yar Ghana ce Bestie safeera matan Ahmed Xm,duk hidima biki dakomai dashige da fitan biki Ahmad da safeera, Rihanna CE kangaba, Rihanna tashige Xm Academy na Ahmad sukayi shakuwa na bala,I ,labari Dake yawo Rihanna classic girl CE tazama budurwan Ahmad Xm, bikinta sauran Yan kwanaki wasu nazargi Ahmed ne zai aureta ,Wasuma since tashigema safeera ne dan ta auri mijinta tunda Ahmed nada kudi.To yanzu safeera da Rihanna ba BestieWanan maiza Akira kwadayi ko cin,AmanaMaganganu Dake ta yawo kenan a TikTok. https://www.tiktok.com/@adijatouahmed3/video/7571626427221576967?_t=ZS-91LeqTC1M6j&_r=1