Saturday, December 6
Shadow
Hukumar ‘Yansanda ta sanar da dalilin da yasa ta kama Omoyele Sowore

Hukumar ‘Yansanda ta sanar da dalilin da yasa ta kama Omoyele Sowore

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya ta sanar da dalilin kama dan fafutuka kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore. Kakakin 'yansandan Najeriya, Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa an kamashi ne saboda saba umarnin kotu na zuwa zanga-zanga guraren da kotun ta haramta yin hakan. Ya bayyana cewa, wadanda aka kama saboda zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu din yanzu jimulla su 14 ne. Yace wadanda suka kama bayan da Sowore ya tsere sun bayyana cewa shine ya jagorancesu zuwa yin zanga-zangar. Yace dan haka rashin kama Sowore zai zama kamar ba'a yi adalci ba kenan. Ya kara da cewa ba zai wuce awanni 24 a wajansu ba, zasu gurfanar dashi a gaban kotu dan a yanke masa hukunci, kamar sauran.
Da Duminsa:An kama Omoyele Sowore a babban kotun tarayya dake Abuja

Da Duminsa:An kama Omoyele Sowore a babban kotun tarayya dake Abuja

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, 'Yansanda a babban birnin tarayya, Abuja sun kama dan fafutuka kuma me rajin kare hakin bil'dama, Omoyele Sowore. An kamashi ne a yayin da yake fitowa daga cikin babbar kotun tarayya dake Abuja inda akewa Nnamdi Kanu shari'a. Rahoton yace 'Yansandan sun saka Sowore a gaba yayin da yake fitowa daga Kotun inda suka ce su wuce office. Bayan da aka yi tirka-tirka Sowore dai ya yadda an tafi dashi. Wani na kusa da Sowore yace dama can 'yansandan sun gayyaceshi amma Azarbabin sune yasa suka zo kamashi.
Ku tashu tsaye ku kare kanku, Babu maganar biyan kufin fansa ko Sulhu>>Gwamnan Jihar Naija, Umar Bago ya gayawa mutanen jihar

Ku tashu tsaye ku kare kanku, Babu maganar biyan kufin fansa ko Sulhu>>Gwamnan Jihar Naija, Umar Bago ya gayawa mutanen jihar

Duk Labarai
Gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya baiwa mutanen jiharsa shawarar su tashi tsaye su kare kansu. Yace matsalar garkuwa da mutane dan neman kudin fansa a jihar ya kai matakin yaki inda yace dole sai an tashi tsaye. Gwamnan yace, ba zai biya kudin fansa ba kuma babu maganar sulhu da 'yan Bindigar yace idan aka rika basu kudi, zasu mayar da abin kasuwanci. Gwamna Bago yace kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kowane dan kasa damar kare kansa da Dukiyarsa.
Kalli Bidiyon:Yanda tsohon shugaban kasar Fransa Nicolas Sarkozy ya fara zaman gidan yari na shekaru 5 bayan da aka sameshi da laifin karbar kudin yakin neman zabe ta hanyar da bata dace ba

Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy ya fara zaman gidan yarin da aka yanke masa na tsawon shekaru 5. An sameshi da laifi ne na karbar kudin yakin neman zabe ba ta hanyar data dace ba. Wannan dauri da aka masa shine irinsa na farko a tsakanin shuwagabannin kasar ta faransa a cikin shekarun bayabayannan. Kalli Bidiyon anan https://www.youtube.com/watch?v=IEWMOqQs2pU?si=wl8g-yvmNRBuwenW
Kalli Bidiyo: Rykhichi ya kunno kai a kungiyar Izala inda aka samu wasu matasan malamai suka gayawa Sheikh Farfesa Sani Rijiyar Lemu maganganu marasa dadi

Kalli Bidiyo: Rykhichi ya kunno kai a kungiyar Izala inda aka samu wasu matasan malamai suka gayawa Sheikh Farfesa Sani Rijiyar Lemu maganganu marasa dadi

Duk Labarai
Rikicin cikin gida ya kunno kai a kungiyar Izala. Malam Ibrahim Matayassara ne ya fito ya ce yana jawo hankali ga Farfesa Sheikh Sani Rijiyar Lemu da cewa ya rika girmama malamai na zamaninsa ya daina tunanin shine ya fi owa ilimi. Sannan Yace shi fadakarwa ce yayi ga Sheikh Rijiyar Lemu ba rashin kunya ba. https://www.tiktok.com/@isah_bello_assalafy_garo/video/7563743936150310164?_t=ZS-90m2FmtZd9l&_r=1 Saidai lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu malamai suka fito suka yi Allah wadai da wadannan kalamai nasa https://www.tiktok.com/@sheikmurtala01/video/7564029374526196999?_t=ZS-90m1xKLFhJo&_r=1
Abubuwa na ci gaba da kankama, Kalli Bidiyon yanda akawa Maiwushirya da ‘YarGuda gwaji a Asibiti

Abubuwa na ci gaba da kankama, Kalli Bidiyon yanda akawa Maiwushirya da ‘YarGuda gwaji a Asibiti

Duk Labarai
Bidiyo ya bayyana inda aka ga yanda akawa Maiwushirya da 'YarGuda Gwaji a Asibiti a ci gaba da shirin aurensu. https://www.tiktok.com/@pharooq_/video/7564102158837091604?_t=ZS-90m17FI9oP3&_r=1 Hakanan an ga sun je ofishin shugaban Hisbah na Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa inda ya fati matakan da za'abi a kai ga auren. Kotu dai tace nan da kwana 90 za'a daura auren.
Kalli Bidiyon: Abin Kunya, wasu ‘yan Najeriya suka rika rokon ‘yan kwallon kafar kasar Africa ta Kudu abinci a jihar Ogun

Kalli Bidiyon: Abin Kunya, wasu ‘yan Najeriya suka rika rokon ‘yan kwallon kafar kasar Africa ta Kudu abinci a jihar Ogun

Duk Labarai
Bidiyon abin kunyar da ya faru a jihar Ogun na ta yawo a kafafen sadarwa inda aka ga 'yan Najeriya na rokon 'yan kwallon kafar kasar Africa ta Kudu abinci. 'Yan kwallon wanda suka je filin kwallo na MKO Abiola dake Abeokuta dan wasa da Remo Stars sun rika jefawa 'yan Najeriyar sauran abincin da suka ci suka rage. Da yawa dai sun yi Allah wadai da mutanen. Kalli Bidiyon anan https://www.youtube.com/watch?v=cq1Y4xEJEDo?si=MlWRJFlqZGtx8RYH