Saturday, December 6
Shadow
Kalli Bidiyo: Tauraruwar Tiktok Habiba Dorayi ta fito ta bayar da hakuri game da Bidiyon da aka ga tana Bhatsaa a ciki wanda ya yadu sosai

Kalli Bidiyo: Tauraruwar Tiktok Habiba Dorayi ta fito ta bayar da hakuri game da Bidiyon da aka ga tana Bhatsaa a ciki wanda ya yadu sosai

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Habiba Dorayi ta fito ta bayar da hakuri game da Bidiyon ta na batsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta. Habiba a Bidiyon data wallafa a shafinta na Tiktok tace hukumar tace fina-finan Kano ta nusar da ita cewa abinda ta yi bai dace ba. Tace dan haka tana baiwa duk masoyanta hakuri kuma hakan ba zai sake faruwa ba.
A karin farko, An ga Sauro a kasar Iceland

A karin farko, An ga Sauro a kasar Iceland

Duk Labarai
Rahotanni sun ce a karin farko an ga Sauro a kasar Iceland. Kasar Iceland dai itace daya tilo da babu sauro a Cikin a tsakanin kasashen Duniya. Dalili kuwa shine kasar na da tsananin sanyi wanda sauro baya iya rayuwa a ciki. Sannan kuma basu da ruwa dake kwanciya sosai wanda shima hakan na taimakawa wajan tara sauro. Saidai duk da haka gashi a karin farko a yanzu an ga sauro a kasar.
Kalli Bidiyo: Mafi yawanci abinda zai kai mutanen Arewacin Najeriya Whuta hakkin bayin Allah ne>>Inji Sheikh Nura Khalid

Kalli Bidiyo: Mafi yawanci abinda zai kai mutanen Arewacin Najeriya Whuta hakkin bayin Allah ne>>Inji Sheikh Nura Khalid

Duk Labarai
Malam Nura Khalid ya bayyana cewa, mafi yawancin abinda zai kai mutanen Arewacin Najeriya wuta, hakkin bayin Allah ne. Malam ya kawo misali da hakkin 'ya'ya akan iyaye inda ya kawo misalin masu haihuwar 'ya'ya su barsu suna watangaririya a titi. https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7563977265688710407?_t=ZS-90ld9ZHi77Z&_r=1
Da Duminsa: Dangote zai sayar da wani sashe na matatar mansa

Da Duminsa: Dangote zai sayar da wani sashe na matatar mansa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Attajiri, Dangote zai sayar da wani kaso tsakanin kaso 5 zuwa 10 na matatar mansa a kasuwar hannun jarin Najeriya. Dangote ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a kafar  S&P Global ranar 20 ga watan October inda yace zai yi hakanne kamar yanda yawa kamfanoninsa na sukari dana Siminti. Dangote yace baya son rike fiye da kaso 65 zuwa 70 cikin 100 na hannun jarin matatar man. Yace a hankali a hankali zai rika sayar da hannun jarin matatar ya danganta ga yanda mutane ke son saye ko kuma yanayin kasuwa. Hakanan Dangote yace yana son kara yawan man fetur din da suke tacewa duk rana zuwa ganga Miliyan 1.4 a kowace rana. Idan hakan ta tabbata, matatar man Dangote zata zama ta daya a Duniya wajan yawan fitar da man fetur inda zata zarta ta kasar I...