Dan Wasa Mbappe Ya Ji Rauni A Karan Hanci A Wasan Da Suka Yi Da Austria
Kylian Mbappe ya ji rauni a karan hanci a wasan farko da Faransa ta yi a cikin rukuni na hudu a Euro 2024, amma baya bukatar tiyatar gaggawa.
Wadda ta yi ta biyu a kofin duniya a Qatar a shekarar 2022 ta yi nasarar cin Austria 1-0, bayan da Maximilian Wober ya ci gida a minti na 38 a karawar farko a cikin rukuni.
An sanar da cewar ba sai an yi wa sabon dan kwallon Real Madrid tiyata da wuri ba, wanda ake fatan zai murmure a kan lokaci.
Hukumar kwallon kafa ta Faransa ta sanar cewar za ta samar da kariyar fuska ga kyaftin din, amma ba ta fayyace ko zai buga wasa na biyu da Netherlands ba.
Mai shekara 25, sai sauya shi aka yi a wasan da Faransa ta yi nasarar cin Austria 1-0 a ranar Litinin.
Ya kuma ji rauni ne sanadiyyar karo da ya yi da kafadar Kevin Danso, lokacin da suka ci...




