Saturday, December 6
Shadow
Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello da EFCC ke bincike kan zargin Satar Naira Biliyan 80 yace shugaba Tinubu ba sai ya je jikar Kogi yakin neman zabe ba, ya ci zaben 2027 a jihar

Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello da EFCC ke bincike kan zargin Satar Naira Biliyan 80 yace shugaba Tinubu ba sai ya je jikar Kogi yakin neman zabe ba, ya ci zaben 2027 a jihar

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tabbaci cewa, ba sai ya je yakin neman zabe ba jihar Kogi. Yace shugaban ne zai yi nasara a zaben shekarar 2027 me zuwa. Ya bayyana hakane a wajan yakin neman zabe inda ake nuna goyon bayan ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kuma gwamna Usman Ododo na jihar kan su zarce a karo na biyu.
Dan Shugaban kasa, Seyi Tinubu ya baiwa ‘yar Fim Kyautar Naira Miliyan 20

Dan Shugaban kasa, Seyi Tinubu ya baiwa ‘yar Fim Kyautar Naira Miliyan 20

Duk Labarai
Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya baiwa 'yar Fim, Sarah Martins kyautar Naira Miliyan 20. Sarah Martins dai ta gamu da fushin hukumomi a Legas inda suka hukuntata bayan da ta dafawa marasa karfi Abinci akan titin Legas. Saidai Dan shugaban kasar ya share mata hawaye ta hanyar bata kyautar Naira Miliyan 20. Lamarin ya dauki hankula sosai inda ake ta cece-kuce da zazzafar Muhawara
Emmanuel Efayeta Kuejubola ya aikawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu budaddiyar wasika inda yake neman ya bashi bashin Naira 12 zai yi kasuwanci

Emmanuel Efayeta Kuejubola ya aikawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu budaddiyar wasika inda yake neman ya bashi bashin Naira 12 zai yi kasuwanci

Duk Labarai
Wani mutum dan jihar Delta me suna Emmanuel Efayeta Kuejubola ya aikawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da budaddiyar wasika inda yake neman shugaban kasar ya bashi bashin Naira Biliyan 12. Yace burinsa shine ya gina gidaje 400 masu dakina 2 a jiharsa ta Delta. Yace idan aka bashi bashin, nan da watanni 36 zai mayar da kudin ya biya bashin. Yace a baya ya taba aikawa Dangote irin wannan wasika amma bai sami amsa ba. Yace yana fatan a wannan karin zai samu amsa daga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Kalli Bidiyon: Idan kuka ganni Ina Saka Hotuna ko Bidiyon Tsyraychi ko kuka ga ina Aikata Alfasha da wani kada wanda ya sake min gargadi ko yace inji tsoron Allah saboda na dade ina rokon a Taimakeni dan Allah babu wanda ya kulani, dan haka zan ci gaba da bada jikina>>Inji Maryam Buzuwa

'Yar Tiktok Maryam Buzuwa ta dauki hankula sosai bayan da ta wallafa wani Bidiyo tana cewa zata ci gaba da nuna tsitaici da kuma bayar da jikinta tana samun abinda take so. Tace dalili shine ta nemi a bata dan Allahu babu wanda ya kulata. Sannan tace kada wanda ya sake ce mata ta daina ko ta ji tsoron Allah. Tace ko Iftihal Madaki bata ga laifinta ba itama kwanannan za'a ganta tare da su Soja Boy din. https://www.tiktok.com/@maryambuzuwa20/video/7552927061925645576?_t=ZS-90eUwmASTDt&_r=1
Da Duminsa: Wasu sojojin Najeriya sun Shirya yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki saidai an yi nasarar kamasu kamin su ida nufinsu

Da Duminsa: Wasu sojojin Najeriya sun Shirya yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki saidai an yi nasarar kamasu kamin su ida nufinsu

Duk Labarai
Rahotanni daga kafar Sahara reporters wanda tace ta samo ta wasu majiyoyi sun ce wasu sojoji sun yi yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki. Sojojin sun shirya juyin Mulkinne ranar 1 ga watan Oktoba ta hanyar harbe shugaban kasar da wasu manyan jami'an tsaronsa sannan su ayyana gwamnatin Soja. Rahoton yace sojoji 16 yanzu haka suna hannu wadanda suka fara daga mukamin Kaftin zuwa Brigadier General bisa wannan zargi. Sahara reporters tace hukumar sojin tace an kama sojojin ne bisa laifuka daban-daban da suka aikata amma ba haka bane gaskiyar lamarin. Majiyar tace an ce sun aikata wasu laifukane kawai dan ba'a so maganar ta fita.
Kalli Bidiyon: Abin takaici ne, mun gama Zhagin wadanda ba musulmai ba da cewa Arnane masu fitsari a tsaye amma yanzu munce Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) shima yana fitsari a tsaye>>Inji Sheikh Nura Khalid

Malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid ya bayyana takaici kan yanda yace ake samun musulmai na Alfahari da Ni'imar Musulunci har suna yin gori da ita. Malam yace ana zagin Wadanda ba musulmai ba da sunan Arna masu fitsari a tsaye sai kuma ga wasu malamai sun bayyana suna cewa, Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ma yana fitsari a tsayen. Malam ya bayyana hakanne a wani Bidiyonsa da yake wa'azi wanda ya yadu sosai. https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7562432407513632007?_t=ZS-90eBwKMq07V&_r=1
Samun Mijin Aure akwai Wahala, ni yanzu ko me mata na samu zan aura kuma zan yi kokari mu zauna Lafiya>>Inji Shahararriyar Mawakiyar Kudu, Tiwa Savage

Samun Mijin Aure akwai Wahala, ni yanzu ko me mata na samu zan aura kuma zan yi kokari mu zauna Lafiya>>Inji Shahararriyar Mawakiyar Kudu, Tiwa Savage

Duk Labarai
Tauraruwar Mawakiyar Kudu Tiwa Savage ta bayyana cewa samun mijin aure akwai wahala. Ta bayyana hakane a wata sabuwar hira da aka yi da ita inda take cewa, ita wanda zai dace da ita sai ya kai shekaru akalla 50. Tace to dole zai kasance me mata kuma a shirye take ta zama mata ta biyu, kuma zata yi kokarin su zauna lafiya a matar mijin nata. Tace tana da girmamawa kuma zata kiyaye duk wasu sharuda da za'a gindaya mata.
Alfashar dake faruwa a yankin Arewa ta zarce duk inda ake Tunani, Wai a Arewa ne za’a kama mutum da mata 3 a dakin Otal ya Rhasu>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Alfashar dake faruwa a yankin Arewa ta zarce duk inda ake Tunani, Wai a Arewa ne za’a kama mutum da mata 3 a dakin Otal ya Rhasu>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana takaici kan yanda yanayin lalacewar tarbiyya musamman da yawaitar zinace-zinace suka yi yawa a tsakanin al'umma. Malam ya bayyana hakane a yayin wa'azin da ya gudanar na Mukhtasar Khalil a masallacin Sultan Bello dake Kaduna Ranar Juma'a. Malam yace Al'ummar Arewa da aka santa da Kunya da kawaici Yau Tiktok yasa mata sun zama marasa kunya. Malam yace a Arewa ne aka samu wata mace tace Minista ya mata ciki ya kuma ki daukar nauyin dan. Yace hakanan a Arewa ne aka samu wani ma'aikacin Kwastam da mata 3 a dakin Otal ya mutu. Yace dole Allah ya jarrabemu.
Dan Najeriya da ya tafi kasar Amurka a Keke ya makale a kasar Guinea Bissau inda yace ya kasa cire kudi daga bankinsa na UBA, ko ruwa saidai a bashi taimako

Dan Najeriya da ya tafi kasar Amurka a Keke ya makale a kasar Guinea Bissau inda yace ya kasa cire kudi daga bankinsa na UBA, ko ruwa saidai a bashi taimako

Duk Labarai
Dan Najeriya da ya tafi kasar Amurka a keke, Emmiwuks ya bayyana cewa, ya makale a kasar Guinea Bissau inda yace ya kasa cire kudi daga asusun ajiyar kudinsa na bankin UBA. Yace ko ruwansha saidai mutane su bashi tallafi. https://twitter.com/NigeriaStories/status/1979140103038480481?t=wlCYKtdKh6Q9cW9HhA3EmA&s=19
Sulhu ba zai taba yin aiki ba, Maganin mutanen nan kawai a Baza musu Whuta>>Shugaban Tsaro, Christopher Musa

Sulhu ba zai taba yin aiki ba, Maganin mutanen nan kawai a Baza musu Whuta>>Shugaban Tsaro, Christopher Musa

Duk Labarai
Shugaban Rundunar tsaron Najeriya, Christopher Musa ya bayyana cewa Sulhu ba zai yi aiki a yaki da 'yan Bindiga ba. Yace kokarin yin sulhu bata lokaci ne kawai, ba zai taba cimma abinda ake so ba. Yace Gwamnatocin jihohin basa basu hadin saboda kowace jiha na da irin salon da take son yin amfani dashi dan magance matsalar. Yace abinda 'yan Bindigar kawai suke so shine Mulki, Kudi, da barzana ga mutane, Kamar yanda Idris4peace ya ruwaito. https://twitter.com/Edrees4P/status/1979163699853115421?t=8rzf_v8fo8yK_ikeoNJ33Q&s=19