Saturday, December 6
Shadow
Kalli Bidiyo: Soja ta baiwa Abokan aikinta maza shawarar cewa, su san irin matan da zasu rika aure, dan wasu matayen sojojub so suke a kaisu yaki a Kshekye su ci gado

Kalli Bidiyo: Soja ta baiwa Abokan aikinta maza shawarar cewa, su san irin matan da zasu rika aure, dan wasu matayen sojojub so suke a kaisu yaki a Kshekye su ci gado

Duk Labarai
Wata soja ta baiwa abokan aikinta shawara cewa, ya kamata su san irin matan da zasu rika aure dan kuwa wasu matan ba da gaske suke son su ba. Ta bayyana hakane a cikin wani Bidiyo data wallafa a shafinta na Tiktok inda take cewa wasu matan na fatan ma a kai mutum yaki ya mutu su ci gado. Kalli Bidiyon ta anan: https://www.tiktok.com/@numcy5/video/7562213981507783943?_t=ZS-90fjbZewzOy&_r=1
Talauci ne babban makiyin dan Adam>>Inji Atiku Abubakar

Talauci ne babban makiyin dan Adam>>Inji Atiku Abubakar

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, Talauci shine babban makiyin dan Adam. Ya bayyana hakane a cikin sakonsa na ranar yaki da Talauci ta Duniya. Yace Talauci na kawo Jahilci, Cutuka, Matsalar tsaro, da rashin Tabbas a rayuwa. Yace saka wannan rana a matsayin ranar yaki da Talauci ta Duniya kira ne ga gwamnatoci da kungiyoyin fafutuka dama duka masu ruwa da tsaki kan a hada hannu dan yakar Talauci. Yace dolene a dauki matakan yaki da Talauci a Najeriya.
Tinubu Mala’ikane wanda Allah ya turo ya gyara Najeriya>>Inji Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello

Tinubu Mala’ikane wanda Allah ya turo ya gyara Najeriya>>Inji Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Mala'ikane wanda Allah ya aiko ya gyara Najeriya. Ya bayyana hakane a wajan yakin neman zaben sake zaben gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Yahya Bello yace Allah ba zai aiko da mala'ika daga sama ya gyara Najeriya ba dan haka Shugaba Tinubu ne mala'ikan. EFCC dai na binciken Yahya Bello kan zargin satar Naira Biliyan 80.
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Kalli Bidiyon yanda Rahama Sa’idu ta yi Khadari wanda tace ya girgizata sosai, Shahararriyar Motarta, GLK ta lalace

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Kalli Bidiyon yanda Rahama Sa’idu ta yi Khadari wanda tace ya girgizata sosai, Shahararriyar Motarta, GLK ta lalace

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu ta bayyana cewa ta gamu da mummunan Hadari. Ta bayyana hakane a shafin nata na Tiktok inda ta wallafa Bidiyon motarta GLK wadda aka gani a cikin rami duk ta lalace. Tace Allah ya tsareta ta tsallake rijiya da baya. Rahama tace rayuwarnan ba tabbas. https://www.tiktok.com/@rahamasaidu2/video/7562548109906054408?_t=ZS-90fDI1hWLoH&_r=1
Sabon Rahoton ya yi bayani dalla-dalla yanda wasu sojoji suka so yiwa shugaba Tinubu juyin mulki, Sun so su aika shugaba Tinubu, Kashim Shettima, Akpabio da Tajudeen Abbas Qhiyama

Sabon Rahoton ya yi bayani dalla-dalla yanda wasu sojoji suka so yiwa shugaba Tinubu juyin mulki, Sun so su aika shugaba Tinubu, Kashim Shettima, Akpabio da Tajudeen Abbas Qhiyama

Duk Labarai
A baya mun samu rahoto daga Sahara reporters cewa an kama wasu sojoji 16 da suka yi yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki. Duk da hukumar sojoji tace sojojin sun aikata wasu laifuka ne na rashin da'a, Saidai Sahara reporters tace juyin Mulki ne sojojin suka shirya amma ake boye maganar. Hakanan kafar Premium times itama ta tabbatar da cewa aojojin sun shiryawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin mulki ne. Hakanan an kamasu ne tun kamin ranar 1 ga watan October, sannan su kusan 20 ne a cewar Sahara reporters Hakanan premium times tace sojojin sun shirya yin juyin mulkinne ranar 25 ga watan October inda suka so kashe ahugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio, dana wakilai, Tajudeen Ab...
Allah Sarki: Ji Yanda matar aure ta yanke jiki ta fadi sumammiya bayan da mijin ta ya saketa a Kotu, Ta kai karane inda tace Alkali ya hana mijin sakinta saboda bata so su ramu amma mijin yace shi baya sonta

Wata matar aure Mulikat Yusuf ta yanke jiki ta fadi sumammiya bayan da mijinata ya saketa a kotu duk da kai kara da ta yi akan kada ya saketa. Matar ta kai mijinta, Ishaq Abdulganiyu kara inda tacewa kotu ta haifa masa yara 6 kuma ita yanzu idan ya saketa bata san inda zata ba. Saidai mijin yace babu ruwansa da ita. A hanyarta ta fita daga kotun ta yanke jiki ta fadi. Saida aka yayyafa mata ruwa ta farfado. Lamarin ya farune a kotun dake Igboro, Ilorin jihar Kwara. Alkalin kotun, Toyin Oluko ya baiwa matar shawara ta je ta lallaba mijinta. An daga ci gaba da sauraren shari'ar har zuwa 5 ga watan Disamba, inda alkalin yace ya basu damar su shirya kamin lokacin ko kuma a ci gaba da shari'a.
Hukumar Sojojin Najeriya ta yi martani kan rahoton juyin Mulki

Hukumar Sojojin Najeriya ta yi martani kan rahoton juyin Mulki

Duk Labarai
Hedikwatar Tsaron Nijeriya Ta Karyata Zargin Yunƙurin Juyin Mulki A wani jawabi da ta fitar don fayyace dalilin soke bukukuwan samun 'Yancin Kai, Hedikwatar Tsaron Najeriya ta musanta jita-jitar da ke yawo kan zargin yunƙurin juyin mulki. A cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Tukur Gusau ya rattaba wa hannu, hedikwatar ta ce an soke bikin samin ƴancin kan ne don bai wa sojojin Najeriya damar mayar da hankali kan yaƙi da suke da ta'addanci da ƴan bindiga, kana da bai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu sararin halartar wani taro mai muhimmanci kan kyautata dangantakar kasa da kasa. Rundunar ta kuma yi ƙarin haske kan binciken da ake ci gaba da yi kan zargin wasu jami'anta 16 da nuna rashin ɗa'a wajen aiki, inda ta tabbatar wa 'yan Najeriya cewa zargin ya dogara ne kan aiyukan soji na ya...
Kalli Bidiyo: Shekaruna 29 amma har yanzu ban yi aure ba, har kudi na kashewa Samari amma har yanzu ba wanda ya fito da niyyar aurena, ina zan saka kaina? Matashiya ta fashe da kuka

Kalli Bidiyo: Shekaruna 29 amma har yanzu ban yi aure ba, har kudi na kashewa Samari amma har yanzu ba wanda ya fito da niyyar aurena, ina zan saka kaina? Matashiya ta fashe da kuka

Duk Labarai
Wannan matashiyar 'yar Najeriya ta fashe da kuka a wani Bidiyo data wallafa inda tace kadan ya rage ta kai shekaru 29 amma har yanzu bata da mijin aure. Ta bayyana hakane a wani Bidiyo ta da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda tace laifin me ta aikata, tace tana da hali me kyau, har kudi take kashewa samari amma har yanzu bata samu mijin aure ba. Wannan Bidiyon nata ya jawo zazzafar Muhawara a kafafen sadarwa. https://twitter.com/dammiedammie35/status/1979443581778825327?t=E8JUTsHz_dy0PccfA-2P8w&s=19
Ashe Maganar Juyin Mulki Gaskiya ce, shiyasa naga manyan kasar Hadda Tinubu sun tafi kasashen waje ta yanda idan an yi juyin Mulkin zasu samu sauki>>Inji Tsohuwar Hadimar Shugaban kasa, Lauretta Onochie

Tsohuwar hadimar shugaban kasa a zamanin Mulkin shugaba Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta bayyana cewa ashe maganar juyin mulkin gaskiyace. Tace shiyasa suka ga manyan kasar hadda shugaban kasa sun tafi kasashen waje ta yanda idan an yi juyin mulkin zasu samu sauki. Ta bayyana hakane a shafinta na X. https://twitter.com/Laurestar/status/1979487065558413410?t=LnL_Po2oag7OFwu1jF5xxQ&s=19 Hakan na zuwane bayan da Sahara reporters ta ruwaito cewa, an kama wasu janarorin soji 16 da suka yi yunkurin yiwa Gwamnatin Tinubu juyin mulki.