Kaduna: Kotu Ta Dawo Da Wani Babban Basarake da El-Rufa’i Ya Tsige
Kotun masana’antu ta kasa da ke zamanta a Kaduna a ranar Litinin din da ta gabata ta yi watsi da tsige babban sarkin Piriga da ke karamar hukumar Lere, Cif Jonathan Pharaguwa Zamuna.
Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Bashir Attahiru Alkali, bayan ya tabbatar da cewa kotun masana’antu ce ke da hurumin sauraron shari’ar, ya ce gwamnatin tsohon Gwamna El-Rufai ba ta bi ka’ida ba wajen tsige sarkin Piriga mai daraja ta uku tare da ayyana aikin ya sabawa kundin tsarin mulki, ba bisa ka'ida ba, rashin adalci, maras amfani, kuma ba shi da wani tasiri.
Kotun ta bayar da umarnin mayar da Cif Zamuna kan karagar mulki tare da biyan duk wani albashi da kuma alfarmar da aka ba shi.
Sannan ta umarci gwamnatin jihar Kaduna da ta biya Cif Zamuna diyyar Naira miliyan 10 saboda tauye masa hakkins...







