Friday, May 23
Shadow

Rundunar Ƴansanda ta rage wa wani ɗansanda matsayi bisa azabtar da wani dattijo a jihar Imo

Rundunar Ƴansanda ta rage wa wani ɗansanda matsayi bisa azabtar da wani dattijo a jihar Imo.

Rundunar ƴansandan jihar Imo ta rage wa wani ɗansanda mai muƙamin Sajan, Anayo Ekezie mukamin sa saboda cin zarafin wani dattijo.

Wani faifan bidiyo na yadda wasu ƴansanda ke cin zarafin wani mutum a kan hanyar Owerri zuwa Aba ya bazu a kwanakin baya.

Kakakin rundunar ƴansanda ta jihar, Henry Okoye, a jiya Laraba, ya tabbatar da cewa an gano ‘yansandan tare da tsare su.

Ya ce an samu ƴansandan uku da lamarin ya shafa, inda ya kara da cewa an rage wa Ekezie mukami zuwa Kofur, yayin da aka ja wa sauran biyun kunne.

Karanta Wannan  Alamomin hawan jini

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *