Wani mutum dan Najeriya ya bayyana cewa, idan aka sakashi wuta iri daya da ta tsohon ministan Sufurin Jiragen sama, Hadi Sirika ba’a masa adalci ba.
Mutumin ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta kuma ya fadi dalilinsa na cewa Hadi Sirika ya saci kudi da yawa.
Hadi Sirika dai na fuskantar tuhume-tuhume kan zargin satar Biliyoyin Naira da suka hada da biliyan 2 wanda ake zargin ya sata shi da diyarsa da surukinsa da kuma Biliyan 19 wadda ake zargin ya sata tare da kaninsa.