Wednesday, February 4
Shadow

Sarakunan Inyamurai sun ce Tinubu ne zabinsu a 2027

Sarakunan yankin Inyamurai sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu alkawarin samar masa akalla kaso 70 cikin 100 na kuri’un da za’a kada a yankunansu.

Sarakunan wanda basaraken Abia, Eze Nnamdi yake jagoranta sun bayyana hakane yayin da suka kaiwa mataimakin kakakin majalisar dattijai, Benjamin Kalu ziyara a gidansa dake Abia

Sunce babban dalilin ziyararsu shine dan mika godiya ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bisa kafa ma’aikatar raya yankinsu.

Sannan sun kuma Godewa Sanata Kalu saboda kokarin da yayi na kafa wannan ma’aikata.

Karanta Wannan  Na yi amanna dari bisa dari Tinubu ne zai sake cin zabe a 2027, saboda babu wani dan takara me karfi da zai iya kayar dashi daga ADC>>Inji Sanata Shehu Sani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *