Shugaban masallatan Harami, kuma sarkin Saudiyya, Salman bin Abdul Aziz Al Saud ya bayar da umarnin gayyatar ƙarin ‘yan uwan Falasɗinawa 1,000 da aka kashe a Gaza a matsayin baƙinsa.
Cikin wata sanarwa da shafin X na Haramain ya wallafa, sarkin ya bayar umarnin ƙarin gayyatar ‘yan uwan Falasɗinawa ne domin halartar aikin hajjin bana.
Dama dai tun da farko sarkin ya gayyaci wasu Falasɗinawan 1,000, inda a yanzu adadin Falasɗinawan da da aka kashe ‘yan uwansu da sarkin ya gayyata ya kai 2,000.