Monday, June 2
Shadow

Saudiyya ta saka tarar riyal 20,000 ga masu yin aikin Hajji ba bisa ƙa’ida ba

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta tabbatar da cewa duk mutumin da aka kama yana taimaka wa mutane wajen yin aikin Hajji ba bisa ƙa’ida ba zai fuskanci tarar riyal 100,000.

Tarar za ta shafi duk wanda da ke ɓoye maniyyatan da ba su da cikakkun takardu a gidajensu, ko nema musu biza, ko kuma yin jigilarsu.

Lokutan da dokokin suka shafa su ne daga 1 ga watan Zulƙi’ida (wanda ya yi daidai da 29 ga watan Afrilu) har zuwa 14 ga watan Zulhijja (10 ga watan Yuni).

Duk mutumin da aka kama yana ƙoƙarin gudanar da aikin Hajjin ba tare da takardun izini ba zai fuskanci tarar riyal 20,000.

Karanta Wannan  Kasar Israyla na shirin Afkawa kasar Ìran da yaki

Sannan kuma za a mayar da shi ƙasarsa tare da hana shi shiga Saudiyya tsawon shekara 10.

Irin wannan tarar za a yi wa duk wanda aka kama da kowace irin biza ta ziyara wadda ta gama aiki yana ƙoƙarin shiga ko ci gaba da zama a garin Makka ko Madina a cikin lokutan da aka bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *