Friday, December 5
Shadow

Serap ta ba wa gwamnan Neja wa’adin janye umarnin rufe rediyon Badeggi FM

Ƙungiyar neman shugabanci na gari ta Serap ta bai wa gwamnan jihar Neja da ke arewacin Najeriya wa’adin awa 48 domin ya janye umarnin rufe gidan rediyon Badeggi FM ko kuma ya fuskanci matakin shari’a.

Cikin wata wasiƙa da ƙungiyar ta aika wa Gwamna Umaru Bago, shugaban Serap Kolawole Oluwadare ya ce rufe gidan rediyon da ke birnin Minna “saɓa wa doka” ne, kuma ya nemi gwamnan ya mayar musu da lasisinsu.

“Toshe bakin masu suka da sunan tsaron ƙasa keta rantsuwar kama aiki da ka yi ne da kuma ɓata sunan Najeriya a idon duniya game da haƙƙin ɗan’adam,” a cewar wasiƙar.

Karanta Wannan  Me ya sa gwamnatin Malaysia za ta hana amfani da motocin CNG?

A ranar Juma’a ne Gwamna Bago ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon na Badeggi FM nan take tare da ƙwace lasisinsa saboda zargin “tayar da fitina”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *