Thursday, February 5
Shadow

Sharrine aka kalamin ban baiwa dana manyan filaye a Abuja ba>>Inji Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa babu gaskiya a maganar da ake yadawa wai ya baiwa dansa filaye a manyan unguwannin Abuja.

Me magana da yawun ministan, Lere Olayinkane ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar ga manema labarai inda yace ko fili daya Wike be baiwa dansa ba.

A baya dai hutudole ya kawo muku rahoton dake cewa kafar Peoplesgazette ta ce ta samu bayanan sirri cewa, Wike ya rabawa ‘ya’yansa filaye a Abuja.

Saidai Wike yace wannan magana karyace da ta fito daga bakin ‘yan jaridar da basu da kwarewa a aikinsu.

Wike yace a ina za’a samu filaye da yawa a Asokoro da Maitama wanda har zai rabawa ‘ya’yansa?

Karanta Wannan  Gwamnan Jihar Abia Senata Alex Otti Ya Ziyarci Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, A Gidan Rumfa Jim Kaɗan Bayan Naɗe-Naɗen Da Aka Gudanar A Yau

Yace idan kuma jaridar tace gaskiyane rahoton data wallafa to ta kawo takarda me dauke da sunan dan Wike dake nuna alamar cewa ya mallaki filaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *