Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A Duniya
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a tarihin duniya.
Alkaluma sun nuna cewa Shehin Malamin, wanda a kwanan nan ya cika shekara dari a duniya — ranar 2 ga watan Almuharram 1444 Hijiriyya — yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani.
A cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, wadanda suka karrama malamin da lambar yabo, Sheikh Dahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya taba samun irin wannan baiwar.
Bayanai sun nuna mashahurin malamain yana da ’ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 da jikoki 199 da kuma tattaba-kunne 12 ne suka haddace Alkur’anin
Yana daga cikin Halifofin Sheikh Inyass
Sheikh Darihu Bauchi ne daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Halifan Darikar Tijjaniyya, bayan wanda ya assasa ta, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.
Yana daga cikin manyan malaman Musulunci a Najeriya, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da Fatawar Musulunci a Najeriya sannan babban jigo ne a Darikar Tijjaniya a Najeriya da ma Afirka.
A zantawarsa da ’yan jarida shekarun baya a Bauchi, Sheikh Dahiru ya ba da takaitaccen tarihinsa, inda ya ce, “Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu — ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu.
To ni dukanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Jihar Bauchi take hade da Jihar Gombe.
“Bayan da aka raba Jihar Bauchi da Jihar Gombe, sai muka zama mu Fulanin Jihar Bauchi ne, a lokaci guda kuma Fulanin Jihar Gombe ne.
Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da ke Jihar Gombe.
“An haife ni ne a watan Janairu”.