
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalam Abubakar me ritaya murnar cika shekaru 83 da haihuwa.
A sanarwar da ya sanyawa hannu ranar Lahadi, Shugaba Tinubu ya bayyana Abdulsalam Abubakar a matsayin mutum me dattako wanda ke son zaman lafiya.
Yace yayi rayuwa me kyau wadda tasa ma’aikatan gwamnati da yawa ke son yin koyi dashi.