Friday, December 5
Shadow

Sojin Nijeriya Sun Tàbbàtar Da Ķàšhè Babban Maķusàncin Bèllò Tùrjì A Yammacin Jiya, Lahadi

A wani gagarumin samame da suka gudanar, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da samun nasarar hallaka babban makusancin shugaban ‘yan Bîndîgâ, Bello Turji, wato Alhaji Shaudo Alku, a ranar 18 ga Mayu, 2025.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan artabu ya auku ne a kusa da makarantar Tunfa da ke ƙaramar hukumar Isa, Jihar Sokoto. Rundunar ta ce an kashe tare da su wasu daga cikin mabiyansu da dama, ciki har da masu hannu wajen kai hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Wannan nasara na daga cikin kokarin da hukumomin tsaro ke ci gaba da yi don murkushe ayyukan ta’addanci da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon Shugaban kasar Nijar, ya dauki nauyin jinyar Malam Nata'ala

Allah ya kara tsare ƙasarmu da kuma bai wa jami’an tsaro nasara akan dukkan masu kawo fitina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *