Thursday, January 16
Shadow

Sojojin Najeriya sun soma fatattakar Làkùràwà daga sassan jihar Kebbi

Rundunar sojin Najeriya ta ƙaddamar da hare-hare kan ƙungiyar ‘yanbindiga ta Lakurawa da ta ɓulla a wasu sassan jihohin Kebbi da Sokoto na arewa maso yammacin ƙasar.

Rahotanni daga yankin ƙaramar hukumar Augie na jihar Kebbi, sun ce sojojin ƙasar sun shiga wuraren da ‘yan ƙungiyar suka kakkafa sansanoni tare da lalata su.

Sojojin sun kuma kori Lakurawan a dazukan ƙaramar hukumar, tare da kuɓutar da wasu daga cikin dabbobin da masu gwagwarmaya da makaman suka sace.

Matakin na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya da ‘yan ƙungiyar suka yi artabu da mutanen gari Mera na yankin ƙaramar hukumar, tare da kashe mutum 15 da sace shanu masu yawa.

Shugaban ƙaramar hukumar Augie, Hon Yahaya Muhammad Augie, ya shaida wa BBC cewa bayan dakarun ƙasar sun soma ƙaddamar da hare-hare kan ƙungiyar, yanzu haka an soma samun gagarumar nasara.

”Ya zuwa yanzu bayanan da muke samu shi ne sojojin Najeriya sun fatattaki ‘yan ƙungiyar Lakurawa a duka faɗin ƙaramar hukumarmu ta Augie, yanzu babu ko mutum guda daga cikinsu da yake cikin kowane yanki na ƙaramar hukumarmu”, in ji shi.

Karanta Wannan  Tinubu ya yi alhinin sojojin Najeriya da suka mùtù a harin Damboa

”Sojoji sun yi ƙoƙari sun shiga daji, sun bi su har inda suke sun fatattake su daga inda suka yi sansani. Bugu da ƙari sun kuma ƙwato shanun da waɗanann mutane suka sace a garin Mera ranar Juma’ar da ta gabata.”

A cewarsa, mutanen yankin sun samu kwanciyar hankali daga barazanar Lakurawa da a kwanan nan ke damunsu.

‘Mun shaida farmakin sojoji kan Lakurawa’

Mutanen garin Mera da ke yankin ƙaramar hukumar ta Augie – waɗanda suka fuskanci hare-haren ‘yan ƙungiyar a baya-bayan nan, har ma Lakurawan suka kashe musu mutum 15 a makon da ya gabata – sun ce sun shaida farmakin da sojojin suka ƙaddamar kan ‘yan bindigar.

Mutanen garin sun kuma ce sun gamsu da matakan da sojojin ƙasar suka ɗauka don ganin sun murƙushe ‘yan ƙungiyar.

Yariman Mera Bashir Isah ya shaida wa BBC cewa tun ranar da Lakurawan suka ƙaddamar da hari kan garin nasu, aka kai sojoji garin domin samar da zaman lafiya.

Karanta Wannan  Karanta Jadawalin Daraktoci 14 da CBN suka kora daga aiki

”Tun ranar da suka ƙaddamar da harin, wallahi a ranar ma da sojoji muka kwana a garinmu, kuma tun daga ranar Litinin suka fara ƙaddamar hare-hare a cikin dazukan ƙauyukanmu, suna fattakar waɗannan ‘yanbindiga.

Ya kuma ƙara da cewa sojojin sun ƙwato duka shanun mutanen garin Mera da ‘yanbindigar suka ƙwace, har ma wasu waɗanda ba na ‘yan garin ba, sojojin sun samu nasarar ƙwato su.

Wani mutum da sojojin suka ƙwato shanunsa daga hannun Lakurawan mai suna Musan Dila ya yaba wa sojojin ƙasar bisa namijin ƙoƙarin da ya ce sun yi wajen tabbatar da tsaro a yankin nasu.

”Dole ne mu yaba wa sojojinmu bisa abin da muka gani na tsaro, kuma jami’an tsaron an suna nan sun aiki ba dare ba rana a wannan yanki namu”, in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa a yanzu hankalun jama’ar garin ya soma kwanciya domin har sun fara fita ayyukansu na yau da kullum kamar girbin hatsi da yankan shinkafa, waɗanda a baya ya ce ba sa iya yi, saboda fargabar Lakuwara.

Karanta Wannan  Me neman kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa, Sunday Igboho ya kaiwa kasar Ingila bukatar ta goyi bayan kafa kasar Yarbawan

Ina Lakurawan suka koma?

Yayin da sojojin na Najeriya ke fatattakar ‘yan wannan ƙungiya ta Lakurawa, abin fargabar shi ne wurin da suka koma.

A baya dai an sha fatattakar ‘yanbindiga daga wasu dazukan jihohin Zamfara da Katsina, amma sai su koma dazukan birnin Gwari da ke jihar Kaduna ko wasu dazukan jihar Neja.

Inda nan ma suke zama barazana ga al’umomin yankin, inda suke kai musu hare-hare tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Lamarin da ya sa tsohon gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufai ya nanata cewa idan ana son kakkaɓe matsalar ‘yanbindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya, to dole ne a ƙaddamar da farmakin bai ɗaya a duka jihohin yankin da ke fama da matsalar tsaro.

Yana mai cewa hakan zai hana ‘yanbindigar yin ƙaura daga dazukan da aka fatattake su domin komawa wasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *