Wednesday, January 15
Shadow

Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin horas da ƴan awaren IPOB a Abia

Rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar dakarun Task Force Tactical Patrol Squad sun kai wani samame a wani sansanin horas da masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) da takwararta ta ESN a unguwar Ihechiowa na ƙaramar hukumar Arochukwu ta jihar Abia.

A yayin farmakin, sojojin sun yi nasarar kutsawa tare da tarwatsa sansanin da kuma lalata dukkan na’urorin horas da mayaƙan da kuma kayayyakin da aka samu a wurin.

Rundunar sojin ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntarta na X.

Cikin wata sanarwa da da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce samamen da sojojinta suka kai wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da ake yi na daƙile ayyukan ta’addanci da ƙungiyoyin IPOB da ESN ke yi, waɗanda ke da alaka da kalubalen tsaro da tashe-tashen hankula da ake fama da su a kan ‘yan ƙasa da ba su ji ba ba su gani ba da kuma jami’an tsaro a jihar.

Karanta Wannan  Tsananin Rashin Tausayi: An Sace Wata Mata Mai Juna Biyu A Hanyar Zuwa Asibiti

Baya ga lalata sansanin ƴan awaren, sojojin sun kuma kai hari kan gine-ginen da ake amfani da su a matsayin maɓoya ga manyan kwamandojin ESN.

Farmakin dai na zuwa ne bayan yadda ‘yan ta’addan IPOB/ESN ke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da hukumomin gwamnati a jihar Abia da ma wasu sassan Kudu maso gabashin Najeriya.

A wani samame na daban kuma, dakarun sojin Najeriyar tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga da maɓoyar ‘yan ta’adda a kusa da Irele da Igbobini da kuma Segbemi Kiribo a yankin dajin Ese-Odo a karamar hukumar Irele ta jihar Ondo.

A yayin aikin share fagen, sojojin sun kwato bindigogi da makamai da dama.

Karanta Wannan  Hotuna: Jami'an tsaro sun kama wannan matar da daruruwan àlbárusan bìndìga za ta kai yankin Yantumaki dake cikin karamar hukumar Dan'musa a Jihar Katsina , tace yunwa ce tasa ta shiga wannan sana'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *