Friday, December 5
Shadow

T-Pain dai ko yara basu tsira daga ukubar gwamnatinsa ba>>Atiku ya soki Tinubu kan Azabtar da kananan yara saboda sun masa zàngà-zàngà

{“remix_data”:[],”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jami’iyyar PDP a shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana Allah wadai da takaici kan yanda gwamnatin shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ta gurfanar da kananan yara wanda ke fama da yunwa da rashin lafiya a kotu bisa zargin cewa sun yi yunkurin kifar da gwamnatin tarayya ta hanyar yin Zanga-zanga.

Hutudole ya ruwaito muku cewa 5 daga cikin yaran dai sun fadi a farfajiyar kotun inda aka garzaya dasu Asibiti.

Atiku a sanarwar da ya fitar da yammacinnan yace an jawo hankalinsa kan lamarin inda yace yana Allah wadai da abinda gwamnatin ta yi.

Yace abin takaici ne yanda ko kananan yara basu tsira daga azabar gwamnatin T-Pain ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ummi Nuhu ta yi bayani kan kyautukan data samu, ciki hadda karin haske kan labarin cewa Hadiza Gabon ta bata miliyan 5

Yace yara suna da ‘yancin a basu kariya sannan suna da ‘yancin yin zanga-zanga saboda nuna rashin jin dadin tsare-tsaren gwamnati domin suma lamarin ya shafesu.

Atiku ya kara da cewa abin ban mamaki ne mutumin dake ikirarin ya yiwa Najeriya fafutuka sannan yawa gwamnatoci da yawa a baya zanga-zangar amma kuma gashi yana murkushe masu yi masa zanga-zanga.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Yanda Itama Sadiya Haruna ta bude sabuwar wayarta kirar iPhone 17 pro max daga kwali

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *