Thursday, June 5
Shadow

Talauci na karuwa a Najeriya, Musamman a kauyuka>>Inji Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa, Talauci na karuwa a Najeriya musamman a cikin kauyukan Kasar.

Bankin yace kaso 75.5 na mazauna kauyuka na fama da Talauci inda suke rayuwa a kasa da layin Talauci na Duniya.

Bankin ya bayyana hakane a rahoton da ya fitar na watan Afrilun shekaar 2025.

A watan da ya gabata ne dama bankin ya bayyana cewa, ‘Yan Najeriya da yawa zasu fada cikin matsanancin Talauci nan da shekaru 5 masu zuwa.

Rahotan yace a biranen Najeriya kuma kaso 41.3 cikin 100 ne na mutane ke rayuwa a kasa da layin Talauci.

Layin Talauci dai an dorashi ne akan Mutum ya rika rayuwa akan dala akalla $2.15 kwatankwacin Naira Dubu 3440 kullun, duk wanda yake rayuwa a kasa da wannan kudi a kullun to yana cikin wanda ake kallo a matsayin Matalauta.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: An daura auren fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara da babbar hadimarsa Aisha Humaira a birnin Maiduguri na jihar Borno. Wane fata kuke masu?

Rahoton yace Talaucin yafi yawa a yankin Arewa inda yankin ke da kason Matalauta 46.5 cikin 100, hakanan yankin kudancin Najeriya na da kason matalauta 13.5 cikin 100.

Rahoton yace Akwai zalinci inda ba’a raba daida na arzikin a Allah ya yiwa Najeriya inda ake baiwa wasu kalilan kaso me tsoka amma wasu na samun kadan koma basu samun komai baki daya.

Hakanan rahoton yace talauci tsakanin kananan yara masu shekaru daga 0 zuwa 14 ya fi yawa inda yake da kaso 72.5 cikin 100.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *