Friday, December 6
Shadow

Tauraruwar Fina-finan Hausa,Asma Wakili ta ajiye mukamin da Gwamnan Kano,Abba Gida-Gida ya bata ta fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC

Mataimakin kakakin majalisar Dattijai, Sanata Barau I. Jibrin ya sanar da komawar Tauraruwar Fina-finan Hausa, Asma’u Abdullahi Wakili zuwa jam’iyyar APC.

Ya wallafa hakane a shafinsa na zada zumunta inda ya yi mata maraba zuwa jam’iyyar APC.

Asma Wakili dai Hadimace ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf saidai ta ajiye mukamin nata inda ta kuma fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.

Karanta Wannan  Kalli yanda wata mata ta kona diyar kishiyarta da wuta saboda taci abinci bata tambayeta ba

Sanata Barau yace Asma Wakili ta sanar da ficewarta daga NNPP a yayin ziyarar data kai masa a Abuja.

Barau ya kara da cewa Asma Wakili ta bayyana ayyukan alkhairi na jam’iyyar APC ne ya jawo ta zuwa jam’iyyar.

Yayi kira a gareta data zama jakadiya ta gari ga Masana’antarta ta Kannywood, Jam’iyyar APC da kuma duka Arewacin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *