
Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Mala’ikane wanda Allah ya aiko ya gyara Najeriya.
Ya bayyana hakane a wajan yakin neman zaben sake zaben gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Yahya Bello yace Allah ba zai aiko da mala’ika daga sama ya gyara Najeriya ba dan haka Shugaba Tinubu ne mala’ikan.
EFCC dai na binciken Yahya Bello kan zargin satar Naira Biliyan 80.