Thursday, June 5
Shadow

TIRƘASHI: Añ bankado Natasha na wasa da hankalin jama’a ne kawai game da zargin Akpabio?

TIRƘASHI: Añ bankado Natasha na wasa da hankalin jama’a ne kawai game da zargin Akpabio?

Daga Ibrahim Jamiu Adamu, Abuja

Da so samu ne ba zan ce uffan game da abin da ke faruwa tsakanin Sanatar da aka tura ta wakilci al’ummar Kogi ta tsakiya Natasha da Shugaban majalisar Sanata Godswill Akpabio ba. Amma bayan dogon nazari sai na gane cewa tabbas wannan turka-turka ta jefa al’ummar da suka tura wannan baiwar Allah ta wakilce su tauye musu hakki.

Ga mai bibiyar lamuran da ke faruwa ya san yadda aka kawo inda muke a wanan batu na zarge-zargen Natasha. A waje na ina ganin ƙarara tana nuna ba ta san darajar abin da aka damƙa mata ba.

Mu fara da yadda ta watsar da haƙƙin wakilcin da miliyoyin mutane suka damka mata, kowa ya ga yadda take ta kalaman ɓatanci don neman tausayar al’umma.

Za a iya cewa tun farko ma ba ita al’ummar Kogi ta tsakiya suka zaba ba amma kotu ta yi hukuncinta daga karshe. Irin wannan barankaɗama da take ta yi a majalisa bai kamata a ganta a majalisar dattawa ba, domin wuri ne da yake cike da natsuwa da sanin ya kamata ga mutanen da suka dace.

Bayan dogon nazari da bibiyar lamuranta sai na gane cewa ‘yar taratsi ce kawai da take neman duk wasu hanyoyi na kusta kai inda ba ta kai ba. Da ace za a yi kuturunka nawa a mazabar Kogi ta tsakiya, ba za a iya samun wasu abubuwan a zo a gani na ci gaba da ta kawo wa wannan yanki ba, illa iyaka tana tunkaho da cewa mijinta ke bata shawara, wanda ko hakan rashin sanin darajar aikinta ne, domin sam bai dace iyalanta su kutsa kai a harkar wakilin da aka tura ta ba.

Karanta Wannan  Maganar Jikan Malam Ta Tabbata: Kalli Bidiyon Direba Gurgu na tuka masu kafa

Ba ma wannan ba, tun bayan da ta bijirewa bin doka da oda a majlisa inda ta nuna rashin ɗa’a ƙarara, take ta dora zargen-zargen cin zarafi (na ƙarya) kan shugaban majalisar dattawa, kuma har yanzu ta kasa bayar hujja daya ƙwaƙƙwara da za ta gamsar da duniya abin da take faɗa.

Gaskiya akwai matukar takaici ganin yadda wannan mata tana take ta beman kauda hankalin jama’a kan rashin kunyar da ta yi a majalisar har ta kai ga an dakatar da ita.

Idan har za a yi magana ta gaskiya ANA CUTAR DA AL’UMMAR KOGI TA TSAKIYA, a yanzu fa kowa na da wakilci a majalisar nan kuma wakilansu na abin da ya dace amma ita banda tata mazabar.

Bayan abij da ta yi sai da ta bi kowace hanya don ganin ta ɗauki nauyin ‘yan banga-bangar siyasa su biya mata bukatu da raina hankalin ‘yan Najeriya, domin kowa ya ga yadda ta dinga bijirewa umarnin hukumomi, ita a tunaninta ta fi karfin a shata doka ta bi? Alal misali, Gwamnatin Kogi ta sanya doka amma haka ta yi kunnen uwar shegu da umarni, Allah ya sa Gwamnan ma yana da dattaku

Karanta Wannan  Ana zargin DPO da yin lalata da karamar yarinya me shekaru 15 da aka tsare a fishin 'yansanda a Katsina

Ga wasu karairayin da ta yi wa al’ummar Kogi ta tsakiya kan abin ke faruwa da ita;

  • Ta ce an kai mata hari a gidansu a Kogi… Ina hujja?
  • Shugaban Majalisa da Gwamnan Kogi da Alhaji Yahaya Bello suna neman halaka ta… Ina Hujja? – Babu!
  • Ta je majalisar dinkin duniya ta tsare karairayi wai ana nemanta da lalata – Nan ma ta kasa gabatar da hujja
  • ⁠Ta ce al’ummar mazabarta ba su da ikon yi mata kiranye. Ka ji wani gatsali

Eh haka ne al’ummar mazabar ki ba su ci nasara wajen yi miki kiranye ba a wannan karon, amma tabbas na san yanzu sun gane yadda za su yi waje road da ke, domin abubuwan da suke faruwa sun nuna bai kamata ki kasance a majalisar dattawa ba, domin ke ɗin ba dattijuwa ba ce.

A kwana-kwanan nan kowa ya ga yadda Dr Sanda C Duru wacce aka fi sani Prof Mbegke ta janye jikinta daga mara mata baya domin yadda ta bankado cewa tana son yin amfani da ita wajen cimma wata manufa da babu daraja a cikinta.

Karanta Wannan  Ba Za Mu Koma Gida Ba Har Sai Taliya Ta Sauko, Vewar Wasu Matasa Masu Źanga-Źànga A Kano

Ciki har da yunkurin bata wasu maƙudan kudade Naira miliyan 200 domin ta yi shaidar zur, wai a yi wa Akpabio shugaban majalisar dattawa kazafin yana da hannu a safarar sassan jikin bil-adama, ita kawai burinta shi ne ganin ko ta halin ƙaƙa sai ta nuna ita ke da gskiya.

Muryoyin ta suna nan suna yawo a soshiyal midiya na ƙulle-ƙullen da take yi amma ta kasa samun nasara domin kuwa Prof Mbegke ta buɗe mata aiki, ta ga cewa ba da ita za a yi wannan zubar da ƙimar ba.

Mu ajiye maganar rikicin a gefe yanzu ma, ni babban damuwa ita ce yadda a wannan karon take can tana tsulla-tsulla tana galantoyi a gari babu wakilcin al’ummar Kogi ta tsakiya. Tabbas a wannan lokacin ne al’ummar wannan mazaɓa ke da na sanin aika wannan mata majalisa

Natasha kin cutar da al’ummar mazabar ki da suka tura ki wakilci saboda ta hanyar rashin ɗa’ar ki har ya shafe su. Ina fatan al’ummar Kogi ta tsakiya za su yi haƙuri na ɗan wannan lokaci kafin lokacin da ya dace a maida mata biki. Akwai mutanen da ya kamata mu kira su da dattawa a wannan yanki.

Natasha ki kawo Hujja kawai idan akwai. Ki daina wasa da hankalin jama’a

Suna na Ibrahim Jamiu Adamu daga Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *