Friday, May 9
Shadow

Wanda suke bani kyauta a baya sune yanzu suke rokona in basu kudi saboda matsin tattalin arziki>>Inji Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya bayyana cewa, wadanda ke bashi kyauta a shekarun da suka gabata a yanzu sune ke neman ya tallafa musu.

Peter Obi ya bayyana hakane a wajan taron Jam’iyyar Labour party din da ya wakana a Abuja.

Yace zasu shiga zabe me zuwa a shirye kuma zasu tsayar da mutane na gari a matsayin ‘yan takara.

Peter Obi ya kara da cewa, matsin tattalin arziki yayi tsanani ta yada wanda a baya suke gayyatarsa yana cin abinci tare dasu amma yanzu sune ke neman ya taimaka musu.

Karanta Wannan  Likitocin Abuja za su tsunduma yajin aiki kan korar ma'aikata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *